Advert
Home Sashen Hausa MUSULMI A KATSINA SUN YI TIR DA KASAR FARANSA

MUSULMI A KATSINA SUN YI TIR DA KASAR FARANSA

MUSULMI A KATSINA SUN YI TIR DA KASAR FARANSA

…Sun nemi a kaurace wa duk kayan kasar

Ahmad Muhammad
@Katsina City News

Musulmi karkashin Kungiyar National Islamic Centre (Muslim Umma), sun yi tir da kasar Faransa da Shugabanta, Emmanuel Macron, sun kuma yi Allah wadai da mujallar nan mai zanen barkwanci mai suna CHARLIE HEBDO.

Musulmin sun yi wannan kira ne a wani taron manema labarai da suka kira a Katsina karshen makon da ya gabata, wanda ya samu halartar Wakilai da ‘yan jarida da daman gaske, wanda aka yi a wurin shakatawa na Al-Dusar da ke Katsina.

Taron, wanda Malam Nura Muhammad Iliyasu, Shugaban Kungiyar Dalibai Musulmi ta Jihar Katsina, ya karanta jawabinsu ga manema labarai.

A jawabinsa ya kawo yadda mujallar CHARLIE HEBDO ta yi kaurin suna wajen cin fuska da mutuncin addinai da kuma yadda suka sake buga wani zanen barkwancin da ya daga hankalin Musulmi kusan miliyan dubu biyu duniya.

Malam Ilyasu ya ce Musulmi na cikin wannan juyayi, sai kuma Shugaban kasar Faransa, ya kara wa wutar fetur, inda ya yi wasu maganganu marasa kan gado na suka ga duniyar Musulunci.

Malam Ilyasu ya kara da cewa, maganar da Shugaban na Faransa ya yi ta fusata duniyar Musulmi, wadda ta jawo aka mai da masa martani mai zafi na kalaman hujja daga kasashen duniyar Musulunci. Da kiran a kaurace wa duk kayan kasar Faransa na dukkan amfani da a kan siya.

Malam Ilyasu ya kara da cewa a kan haka ne mu Musulmi daga Katsina muka bi sauran sahun ‘yan’uwanmu na duniya muke kira ga isar da sakon gargadi mai girma ga wannan mujallar ta dakatar da mugun aikin tana cin fuska ga Musulmi da Musulunci.

Ya ce; “Gargadi ga Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron cewa ya zama Shugaba ne mai hangen nesa da hada kan al’umma, ba magana ta haddasa fitina ba.

“Kira ga duk al’ummar Musulmi a ko’ina suke su kaurace wa kayan da ake yi daga kasar Faransa, wadanda ake sayarwa a duk a duniya don kasar ta samu kudin shiga. Har Macron da kasar Faransa su yi nadamar abin da suka yi.”

Sai dai Malam Iliyasu ya yi kira ga duk al’ummar Musulmi da kar su dau doka a hannunsu, amma su bar hukumomin kasashen da kungiyoyin Musulmi na kwarai su bi kadin lamarin.

Sannan ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta kare martaba da darajar addinin Musulunci kar su bari wani ya ci fuskar Musulmi da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Har yanzu: Gwamna Masari na Alhinin Rasuwars Kwamishinan Kimiyya Rabe Nasir

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara bayyana rasuwar Dokta Rabe Nasir a matsayin babban rashi duba da yadda yake da jajircewa tare da sadaukarwa...

Katsina lawyer in court over alleged cheating,forgery, impersonation

A Funtua based Company in Katsina state, NAK International Merchant has dragged a Lawyer, Barrister Mahdi Sa'idu to court over alleged cheating, forgery and...

The YOUTHS ASK YAHAYA BELLO FOR PRESIDENT MOVEMENT (YAYBP) under the Leadership of their Founder/National Coordinator Alhaji Ibrahim Muhammad on Saturday 15th January, 2022...

The movement, which said the gesture is part of its efforts to alleviate the sufferings of the less privileged in the society through its...

Bin Sa’id Tsangaya Model School Ta Yi Bikin Saukar Dalibai.

Daga Auwal Isah. A karon farko, Makarantar hardar Alkur'ani mai tsarki ta " Bin sa'id Tsangaya Model School " da ke a unguwar Tudun 'yan...

Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Kwamishina Rabe Nasir A Jihar Katsina

Ziyarar Da Jigon Jam'iyyar APC Na Kasa, Tsohan Gwamnan Jihar Legas, Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo A Jihar Katsina, Domin Yin Ta'aziyyar Rasuwar...