A farkon ƙarni na 18, an yi wani malami a Katsina mai

Suna Malam Muhammadu bn Muhammad al-Katsinawi
wanda ya shahara a wajen shekarar 1732.
Wannan masani ya karantar, ya kuma yi wallafa ta littattafai da yawa cikin Larabci. A cikin littattafan nasa akwai wani mai suna ‘ Bahajat al-Afaq’ wanda ya ƙunshi bayani kan ilmin taurari, da na sufanci da na lissafi.
Dr. Hassan Ibrahim Gwarzo yayi nazarin wannan littafi, ya bayyana abin da sashin ilmin ya ƙunsa, watau ana yin amfani da ilmin lissafi ne wajen danganta baƙaken Larabci da lissafi. Kowane baki na larabci an ba shi darajarsa a alkaluman lissafi (hisabi) kamar yadda yake a hoto:
Muhimmancin irin wannan lissafin shi ne ana iya shirya
wata kalma guda daya, ko biyu, ko fiye, sannan a zo a bi
darajar kowane babi na cikin kalmar ko kalmonin, a tara
yawan darajojin, sai a sami jimla mai adadin wata shekara
da aka yi wani abu a cikinta.
Wannan shi ne ake kira RAMZI. Masu rubuta waƙoki sun fi sarrafa ramzi. Musamman wakoƙin su Mujaddadi Shehu Usman dan Fodiyo, da na Muhammadu Bello, da na Abdullahi Fodiyo, da na Isan Kware, sukan ƙare da wadansu baitoci masu kalmomin ramzi, watau kalmomin nuna shekarar da aka wallafa waƙokin.
Irin wannan lissafi yana taimakawa wajen fitar da shekarar wallafar wadannan waƙoƙi.
Misali, a cikin wakar nan ta Shehu Usmanu mai suna Tabban Hakikan wadda lsan Kware ya yi wa tahamisi, akwai baiti na 47 wanda yake cewa:
Nan waƙag ga tac cika ai fa ramzi,
JAMMU RUSHDIN ku lura tabban hakikan

Wadannan kalmomi na JAMMU RUSHDIN sun kunshi
haruffan fitar da hijirar da aka wallafa wakar, (3+40+200+1000+4), jimilla 1247hijiriyya (1832 miladiyya)
Sadiq Tukur Gwarzo ya ciro daga littafin HAUSA A RUBUCE: Tarihin rubuce-rubuce cikin Hausa na marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here