Home Uncategorized Muryar matasan Facebook sunyi gagarumin taro a Kano

Muryar matasan Facebook sunyi gagarumin taro a Kano

Daga Yusuf Hamisu

Wannan shekararma dai kamar yanda aka saba shahararren group dinnnan na sahar social media mai suna muryar matasa sun kara gabatar da taronsu na sada zamunci wanda sukema lakabi da suna taron gani da ido, karo na uku ajahar Kano, sama da mutane 300 ne suka halarci taron.
.
Taron ya gudanane aranar lahadi 25/07/2021 wanda yazo daidai 15/12/1442AH.
A babban dakin taron dake toursim camp daura da central hotel kano kusada secretaries din nasarawa local government.

A taron ma kamar yanda suka saba sun gabatar da muhimmaan abubuwa kama daga tattaunawa akan rayuwar matasa dakuma abinda matasa ya kamata su kasance acikin al’ummah dakuma cigaba da koma baya da matasa zasu iya kawoma Al’ummah,
Sannan kamar kowace shekara suna sauke tsaffin shuwagabanninsu dasuka kwashe tsawon shekara guda suna jan ragamar gidan wanda Ustaz yusuf khamsi katsina ya jagoranta amatsayin chairman tare da mukarrabansa.
Inda suka maye gurbinsu da zabbin shuwagabannin da aka zaba wata biyu dasuka gabata kafin taron karkashin jagorancin sulaiman Abdullahi dabai wanda shine amatsayin chairman maici yanzu tare da mukarrabansa.
.
Sannan ayayin taron an kaddamar da gidauniya mai zaman kanta wato (MURYAR MATASA FOUNDATION).
makirkirin dandalin kuma mai jagorantar gidauniyar, Ayayin zantawarsa da manema labarai yace sun kirkiri wannan gidauniyane domin ribatar haduwarsu ta social media ta hanyar hada karfi da karfe wajen taimakon kai da kai dakuma taimakama Marasa lafiya gajiyayyu, marayu, marasa galihu da tallafi na rayuwar yau da kullun, ya kara dacewa gidauniyar ba a wannan taron kadai suka fara budetaba yace sunfara budetane ataronsu na shekarar data wuce wanda sukayishi a MUNAJ EVENT CENTRE dake daura da fatima shema estate acikin birnin Katsina ,
Yace sun samu nasarori sosai wannan yasa a duk shekarar dasu kai taron wata jaha to zasu kaddamar da bude wannan gidauniya reshen wannan jahar.
Sannan yayi bayanin hanyoyinda sukebi domin samo kudaden da kayayyakin dasuke wannan aikace-aikace na wannan gidauniya inda yayi bayani cewa suna hada kudadenne isu-isu mai taro mai sisi,
Amma yace nan gaba sunada burin fitar kokuma tallata wannan kyakkyawan aiki wajen mutanen dasuka kamata wajen tuntubar masu Hannu da shuni wadansa sukasan sunada ruhin taimako da yan’ siyasa masu burin ganin Al’umma taci gaba

Maigirma founder shamsuddeen sa’eed mu’az yace insha Allah sannu ahankali Aikinsu zai kai lungu da sako na kasarnan.
.
Alokacin taron kuma Ankarrama wadansu shugabananni wadansa suka jajirce wajen zama sahun gaba wajen bawa wannan dandali dakuma gidauniyar wadda tasamo asali daga dandalin cigaba
Wadannan mutanedai sun hada da
Chairman mai barin gado ustaz yusuf khamis katsina, da chairlady Asma’u adamu adamawa, Da sakataren watsa labarai Halima Abdullahi daga kaduna,
Saikuma shi kanshi mai gayya mai aikin wato founder shamsudeen sa’eed mu’az.

Alokacin taron anci ansha anyi nishadi anyi zumunci, daga karshe aka dauki hotuna na tunawa da juna.
Taron yafarane daga karfe tara na safe zuwa karfe biyu na rana
Sannan membobinda suka hakarci taron sun fitone daga sassan jahohi da dama kamarsu,
Adamawa, Gombe, Bauchi, sokoto, zamfara, jigawa, Yobe, kaduna, katsina, dakuma kano da kewaye.

Anyi taro antashi lafia kowa yakoma gida lafiya yanamai farinciki tare da kewar yan’uwa.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here