Shugaban Ma’aikatan Fadar Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal ya bayyana cewa shirye-shiryen gwamnatin jihar Katsina sun yi nisa domin ganin an gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar Katsina don ganin an samu zababbun Shugabannin kananan hukumomi da kansilolinsu.

Alhaji Muntari Lawal kuma Madugun Katsina ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattauna wa ta musamman da Blueink News Hausa a gidansa dake kan titin Kangiwa a cikin garin Katsina a jiya Talata.

Madugun Katsina ya ci gaba da cewa gudanar da zaɓen kananan hukumomi talatin da huɗu da kansilolinsu na cikin alkawurran da gwamna Masari ya dauka a lokacin yaƙin neman zabensa na 2015 da 2019 don haka kusan ya zama wajibi kafin gwamnatin nan ta kare mu ke koƙarin ganin an gudanar da zaɓukan don samu zababbun Shugabannin a matakin karamar hukuma.

Shugaban Ma’aikatan ya ci gaba da cewa duk da kalubalen da jihar Katsina ke fuskanta, amma za mu tabbatar mun gudanar da zaɓukan nan gaba kadan. Mun kusa sanya ranar da za mu gudanar da zaɓen kuma muna dab da sanar wa al’ummar jihar Katsina wannan rana da zaran mun kammala shirye-shiryen da muke cikin yi yanzu haka, muna kara ba su hakuri saboda askin ya Zo gaban goshi!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here