Zaharaddeen Mziag @Katsina City News                  10/12/1444-20/7/2021

Sheikh Abdul’ahad Sheikh Ibrahim Niasse

Wata Kungiya me Suna In Niass Foundation, a karkashin Jagorancin ɗan Sheikh Ibrahim Inyass, Sheikh Abdul’ahad Sheikh Ibrahim Inyass R.A ya yanka Shanu guda ɗari bakwai domin rabawa al’umar jihar katsina,

Kamar yanda Katsina City News ta zanta da shi, Sheikh Abdul’ahad ya bayyana cewa; “Muna gudanar da wannan rabon naman a duk shekara, muna bi jihohi-jihohi, kamar yanda bana rabon ya faɗo a Jihar katsina, kamar yanda kuke gani tun safe muke ta aikin yanka shanu ana rabawa jama’a daga ko ina cikin jihar Katsina kuma ga wasu can yanzu haka cikin aikin su ake ba a gama yankawa ba”, Sheikh Abdul’ahad ya kara da cewa; “kuma Alhamdulilah duk da cinkoso da gajiya amma munyi cikin nasara da taimakon Gwamnan jihar katsina, da jami’an tsaro, kuma zan miƙa godiya ta ga Dikko Umar Raɗɗa da ya taimaka sosai har abin yazo Katsina Allah yayi mashi Al’barka, Allah ya saka masa da Alheri”

Wakilanmu na Katsina City News sun zagaya ganewa Idanun su yanda rabon naman shanun ke gudana a cikin Filin wasa na Muhamad Dikko (Muhamad Dikko Stadium) inda suka ga mutane fiye da dubu goma da suka zo amsar naman, tun karfe takwas na safiyar Talata ake aikin har zuwa yamma inda aka rabawa mafiya yawa daga talakawan da suka samu katin shedar amsa dama wadanda basu da katin.

Mun dauko maku Bidiyon yanda rabon naman yake gudana da hira da Shehi, akan yanda tsarin rabon ya kasance. Sai ku ziyarci tashar mu ta YOUTUBE wato Katsina City News TV.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here