Mutanen yankin Sabon Birni a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya sun ce ƴan bindiga sun mamaye yankinsu wanda ya tilasta wa mutane da dama tsallakawa zuwa Nijar.

Ƴan majalisar biyu da ke wakiltar yankin na Sabon Birni ta arewa da kudu sun shaida wa BBC cewa yankin nasu ya koma hannun yan bindiga domin babu jami’an tsaro.

Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa honorabul Aminu Boza ya ce: “kananan hukumomin Isa da Sabon Birnin a yanzu suna ikon yan bindiga, don mahara sun tarwatsa sansanonim jami’an tsaron hudu da a ke da su.

A nasa ɓangaren, dan majalisar dokokin mai wakiltar Sabon Birni ta Kudu honorabul Sai’du Ibrahim ya ce ”ɓarayin da a ka koro daga jihohin Zamfara da Katsina sun dawo Isa da Sabon Birni, kuma Sama da gari 500 a yankin sun watse sun yi Nijar.”

Ikirarin ƴan majalisar majalisar na zuwa yayin da rahotanni suka ce yan bindigar sun hallaka jam’ain tsaro 17 da fararen hula biyu a wasu jerin hare hare da suka kai wasu garuruwa a karamar hukumar Sabon Birnin a karshen mako.

Sai dai kwamishinan tsaro na jihar Sokoto Kanar Garba Moyi mai ritaya wanda bai musanta harin ba, ya ce jami’an tsaro ne ke a da alhakin ba da bahasi game da abin da ya faru da ma’aikatansu.

Ya ce: ”Mun samu labarin harin kuma hare-haren da ake kai wa ƴan bindiga a Zamfara da Katsina idan ba a ɗauki rin matakin ba a jihar Sakkwato ba dole ne su tsallako. Yakamata a ce a dauki yakin bai daya a yi musu kofar rago.”

Sabon Birni na cikin yankunan Sokoto da aka katse hanyoyin sadarwa kamar yadda aka ɗauki matakin a jihar Zamfara da wasu yankuna na Katsina domin magance matsalar ƴan bindiga.

Katse layukan salula na tasiri a Zamfara – Bello Matawalle

Ƴan majalisar biyu na Sabon birni sun ce an afkawa garuruwa biyar da suka hada da ƙauyen Kangara da Katsira inda suka kashe mutun hudu suka jikkata wasu shidda da yanzu haka ke jinya a asibti.

Maharan sun kona mutum biyu a garin na Gangara a lokacin da suka buya cikin rumbun adana abinci.

Aminu Boza ya ce ” Maharan sun cinna wa rumbun wuta da mutanen a ciki, don yanzu haka ina tare da gawawwakin a asibiti duk sun kone gaba daya.”

Ya kara da cewa abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne ” babu sadarwa tun da an yanke network, saboda haka ba mu san ma halin da yankin yake ciki ba a halin da a ke ciki.”

” Hukuma babu ta yanzu ” inda mu ke da sansanonin jami’an tsaro an zo an kashe wasu an kora saura a anguwar Lalle. Saboda haka babu ko da soja daya a anguwar lalle.”

” Yanzu kuma Damaga an kashe jami’an tsaro 17 yanzu haka ina tare da gawawwakin a asibiti”. Inji Aminu Boza.

Dama a baya masana sun yi gargadin cewa matsawar hukumomin ba su hada kai wurin yakar yan bindigar a wadannan jihohi ba, ba shakka yakin zai bar baya da kura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here