Advert
Home Sashen Hausa MUN GANI A KASA A HUKUMAR KASROMA ~~~Cewar Alhaji Salisu Mamman CONTINENTAL

MUN GANI A KASA A HUKUMAR KASROMA ~~~Cewar Alhaji Salisu Mamman CONTINENTAL

A ranar 18 ga watan Oktoba ne na shekarar 2021 wata Kungiya mai zaman kanta da ake kira “Mun Gani A Kasa” ta shirya walimar cikar shekaru biyu da jagoranci injiniya Surajo Yazid Abukur a hukumar KASROMA tare da taya sabbin zababbun Shugabanin Jam’iyyar APC murnar rantsar da su.

A wajen taron an yi hudubobi ga Shugabanin Jam’iyyar da kuma shugaban hukumar na KASROMA. sakataren wannan kungiya ya bayya na irin yadda kungiyar ta samo asali da kuma muhimman ayyukan da kungiyar ta wanzar daga kafa ta zuwa yau.

Shima Sakataren Jam’iyyar APC na jiha Malam Shitu S Shitu yayi jawabin godiya a madadin zababbun Shugabanin Jam’iyyar tare da Jan hankalin mutane wajen yin abin da ya dace in an basu jagoranci Kamar yadda Injiniya Surajo Yazid Abukur ke kamantawa.

A nasa jawabin shugaban rukunin kamfanonin Continental Alhaji Salisu Mamman Continental ya bayyana cewa duk wanda ke jihar Katsina a bangaren hukumar KASROMA ya Gani a Kasa ba labari ba na irin ayyukan da hukumar ta shimfida.

Da yake jawabin godiya shugaban Jam’iyyar ya bayyana makasudin shirya walimar da kuma irin nasarorin da ya samu a cikin shekaru biyu da yayi a bisa Jagorancin hukumar KASROMA tare da kawo misalin wasu ayyukan da hukumar ta aiwatar a cikin shekaru biyu na jagorancinsa.

Walimar ta samu halartar mamyan mutane mabambanta da suka hada da shugaban Jam’iyyar APC na jiha Alhaji Sani Ahmad Aliyu Daura da Sakataren Jam’iyyar Malam Shitu S Shitu da Danmajalissa mai wakiltar karamar hukumar Rimi hon. Abubakar Suleiman Korau da mai ba gwamna shawara bangaren siyasa Hon. Kabir Shu’aibu da tsohon Danmajaly mai wakiltar Rimi Hon. Nasiru Ala Iyatawa da sauran su dama.
An tashi taron lami lafiya bayan an ci an sha.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...