Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara biyan tallafin korona na Survival Fund ga ƙananan ƴan kasuwa.
A shafinsa na Twitter, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an fara biyan mutum 101,567 kuɗaden tallafin na wata wata daga kasuwanci 16,253.
Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da shirin ne domin tallafi ga matsakaitan masana’antu naira biliyan 75, don ƙarfafa musu bayan iftila’in annobar korona.