Advert
Home Sashen Hausa Mun bawa 'yan gudun Hijirar Shimfida Kayan abinci fiye da Buhu 890......Zamu...

Mun bawa ‘yan gudun Hijirar Shimfida Kayan abinci fiye da Buhu 890……Zamu sake kai wasu a cikin azumin nan… Hon. Sani Danlami-

Mun bawa ‘yan gudun Hijirar Shimfida Kayan abinci fiye da Buhu 890……Zamu sake kai wasu a cikin azumin nan… Hon. Sani Danlami-

Kwamishinan Wasanni da Walwalar jama’a na jihar Katsina. Hon. Sani Aliyu Ɗanlami

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

A ranara Lahadi 4/4/2022 Hon. Sani Aliyu Ɗanlami, Kwamishinan Wasanni da Walwalar jama’a na jihar Katsina, ya yi karin haske dangane da irin Tallafin da suka kaima ‘yan gudun hijira na ƙaramar Hukumar Jibiya wadanda suka fito daga yankin Shimfida

Hon. Ɗanlami yace. “Tabbas Al’umar garin Shimfida suna cikin mawuyacin hali, kuma abin a tausaya mawa ne, saboda halin da suka tsinci kansu na harin ‘yan bindiga, suna zaune a garinsu cikin kwanciyar hankali, da raba tsaka sojoji suka bar garin wanda har kawo yanzu bamu san dalili ba.” Inji Sani Ɗanlami.

Kwamishinan ya tabbatar ma Jaridun Katsina City News cewa, bayan sun samu labarin kwashe jami’an tsaro daga garin na Shimfida Gwamnan Katsina ya nuna damuwarsa matuka wanda har ya kira Shugaban Sojojin da ke kula da bangaren tsaron sukayi magana. Ɗanlami ya ce “wanda har yanzu ni ban iya sanin dalilin sojoji na barin garin na shimfida ba bayan sun kwashi fiye da shekaru biyu suna ba garin kariyar tsaro.”

A bangaren bayar da Tallafin kayan masarufi kuwa Hon. Kwamishina ya tabbatar ma jaridun mu, cewa daga lokacin da Ibtila’in ya faru zuwa yanzu, da umarnin Gwamnan Katsina Aminu Masari, a karkashin Ofishin sa sunkai ma ‘yan gudun hijira manyan Buhunnan Masara guda dari biyu da tamanin 280, Shinkafa Buhu ɗari biyu da goma 210, buhun Dawa ɗari biyu da hamsin buhun Gero ɗari da hamsin, da kananan buhunnan garin ɗanwake fiye da ɗari biyu.

A bangaren kayan kwanciya Ɗanlami yace sunkai tabarmi guda dubu biyu da ɗari shida 2600  bargunan rufa guda dubu biyu 2000, hatta kofuffuka da filattai sunkai fiye da guda dubu biyu.

Honarabul Ɗanlami yace basu tsaya anan ba sai da suka gano wasu kauyuka a jamhuriyar Nijar inda Mutanen Shimfida suke, suka je can ma suka kai tallafin.

Honarabul yace a cikin wannan wata na Ramadan ma sun shirya zuwa dukkanin inda Matsalar tsaron nan ta shafa, irin su Jibiya, Safana, Danmusa, Batsari, Faskari da Ƙanƙara domin su raba kayan abinci, wannan na daya daga cikin Ayyukan Ofishin sa, kuma sunayi daidai gwargwado. injishi.

Da wakilin mu yake tambayar sa akan tanadin bangaren Lafiya na masu gudun hijirar Kwamishina yace, basu samu wani korafi na Matsalar rashin lafiya ba, kawo yanzu, amma duk da haka zasuyi tuntuba, kuma zasuyi abinda ya dace, saboda sai da lafiya ake iya cin abincin da ake kaiwa.

A karshe Kwamishinan Wasanni da Walwalar jama’a yayi kira ga sauran al’uma da a sanya jihar Katsina addu’a da kasar baki daya bisa wannan jarabawa da ake fama da ita, su kuma masu gudun hijira suyi kara hakuri da yardar Allah, Allah zai kawo karshen wannan musiba, kuma Gwamnati tana iyakacin kokarinta.

Munada Cikakkiyar Tattaunawar ta Video 📸 a shafin mu  yanar gizo www.katsinacitynews.com

Ku sauke manhajar mu ta Playstor a wayoyin ku, zakuga dukkanin Shirye-shirye mu.

 

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

KUDENDAN POWER STATION AND MANDO SUBSTATION PROJECT REACHED FINAL STAGE OF COMPLETION #PositivefactsNG

The federal government is working tirelessly to complete Kudendan power station and Mando substation in Kaduna state, the state minister of power Engr. Sale...

MATSALOLIN TSARO: Gwamnatin Zamfara tabawa duk dan jiharta damar Mallakar Bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Bai Wa Ƴan Jihar Damar Mallakar Bindiga don kare kansu daga harin ƴan bindiga Gwamnatin Zamfara da ke arewa maso yammacin...

NIMET Installs Message Dissemination Platforms At Abuja, Kaduna, P/H Airports #Positivefacts

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02SkXT7vgAdTkuHz5gW6EaSFt3qZoc4hVMtBMXRMw6SzFv1da5ujPAsEmWyd535tYgl/ Nigerian Meteorological Agency (NiMET) has procured and installed seven automatic message dissemination platforms at Abuja, Kano, Lagos, Maiduguri, Kaduna, Enugu, and Port Harcourt airports. The...

FISHERIES PROJECT CREATES JOBS TO OVER TEN MILLION NIGERIAN #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid0Gc6v3B4e1KT8u7qGbmcMUofbzSaejnB1PTcdjHrBSUaUtQA28bQNeQ3qgLAnhBfzl/The federal government under the leadership of president Muhammadu Buhari, GCFR, has create over ten million jobs to Nigerian through fisheries project, the honourable minister...
%d bloggers like this: