Alhaji Isah Muhammad Ashiru tsohon dan Majalisar Jihar Kaduna ne, kuma ya taba zama dan Majalisar Wakilai, kafin ya yi takarar neman zama Gwamna Jihar Kaduna a zaben shekarar 2019 a Jam’iyar PDP. A zantawarsa da Aminiya ya zargi gwamnatin APC a jihar kan yadda take tafiyar da mulkinta inda ya ce mulkin soja ake yi a jihar ba dimokuradiyya ba:

Me kake ciki tun bayan faduwarka zaben 2019?

Bayan zaben 2019 na yi tunanin komawa gona da harkar kasuwanci na saye da sayarwa. Tun zuwan wannan gwamnati, sai na ga lokaci ne da zan zauna da iyalaina in huta na wani lokaci.

Amma daga wancan lokaci zuwa yanzu jam’iyarmu ta yi nasarar gudanar da zaben
shugabanninta da za su tafiyar da harkokinta.

Me ya sa kake ji ya jawo ka fadi a shekarar 2015 da 2019 da ka fito takarar Gwamna?

A shekarar 2015 tun a zaben share-fage na fadi, inda Malam Nasir El-Rufa’i ya yi nasara a APC, na kuma ci gaba da zama a jam’iyyar har kafuwar gwamnati. Amma suna ganin ba mu da amfani, saboda haka ba ni da wani zabi, sai na bar jam’iyyar, na dawo Jam’iyyar PDP da kowa ya san ni a cikinta, jiga-jigan jam’iyyar ne suka nemi in dawo gida.

A Lokacin zaben share-fage a PDP na samu nasara a cikin mutum tara, kuma kuri’ar da na samu ta ba ni mamaki matuka sannan abokan takarata nan take suka karbe ni, na kuma yi musu alkawari yin aiki tare da su. Ni na san mun ci zabe a shekarar 2019, amma duk abin da ya faru ya zamo tarihi yanzu, kuma ban yi da-na-sani ba.

Akwai maganar da ake yi cewa an ki zabenka ne saboda kana da saukin kai. Ina gaskiyar zancen?

Ba sai na kasance marar mutunci ba, kafin in nuna wa mutane ina da zafi. Kuma ina amfanin yin zafi ga jama’ar da za ka shugabanta? Me ya sa zan zama mai zafi bayan gwamnati ta mutane ce? A matsayin Gwamna, ba ni kadai zan mulki jihar ba.

Matsalar da muke fama da ita, shi wannan Gwamna ba ya neman shawarar kowa a jihar. Shi ba mutum ne mai sauraren mutane ba.

Yanzu mulkin da ake yi a Jihar Kaduna, ya yi kama da mulkin soja, abin da ake so kawai shi ne ka yi biyayya ba tare da yin tambaya ba. Wannan ba mulkin
dimokuradiyya ba ne.

Ba sa son a fadi laifinsu, kuma ba sa sauraren mutane saboda suna tunanin sun fi kowa sani. Tsare-tsaren da APC take gudanarwa a matakin jiha da tarayya abubuwa ne da ba sa yi wa mutane dadi.

Allah ne kawai zai ceci kasar nan daga matsalolin da ake ciki a yanzu, matsalar ita ce a matakin tarayya babu wanda za ka nuna a matsayin jagora. A Jihar Kaduna ma abin da sauki tunda ana ganin El-Rufa’i a ko’ina da za a iya nunawa.

Ke nan kana zargin jam’iyya mai mulki a kan duk abin da yake faruwa a kasar nan?

Sun samu mulkin ne a lokacin da ba su yi tsammani ba, kuma ba su san za su iya cin zabe ba, shi ya sa ba su shirya wa aikin ba. Sun samu mulkin amma sun rasa
yadda za su tafiyar da shi.

Duk ayyukan da suke akwai son rai na wadansu mutane kadan daga cikinsu, don amfanin kansu kurum. PDP ta mika mulki lokacin man fetur yana Naira 67, amma a yau farashin da suke tunanin mayarwa shi ne Naira 385 a kan kowace lita, ci gaba muke yi a haka? Ana sai da Dala lokacin da aka mika musu mulki a kan Naira 215, kwana biyu da suka wuce, Dala ta kai Naira 503.

A Kaduna sun yi alkawarin daukar ma’aikata da rage talauci, wane yanayi ake ciki yau a Jihar Kaduna? Ku dubi yadda wani kawai yana zaune a ofishinsa, a matsayin shugaban ma’ aikata, amma ya kori malaman jami’a don sun shiga yajin aiki. Yaya za ku kwatanta wannan yanayi da lokacin mulkin PDP.

Jami’ar Jihar Kaduna, PDP ce ta gina ta, saboda bai wa ’ya’yanmu damar yin karatu da kudi kalilan. Amma a yanzu fa? An samar da ayyukan yi ga mutanenmu da yin nazari don ci gaba. Me APC suke yi a yanzu idan aka kwatanta da abin da muka yi? Ina ba wa Gwamna shawara ya dubi baya, zuwa yanzu don samun zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here