Kungiyar tuntuba ta Dattawan Arewa (ACF) ta bayyana shugaba Buhari a matsayin abin kunya ga Arewa, kasancewar ya gagara komai kan matsalar tsaro da kasar ke fuskanta, musamman arewacin Najeriya.

Mr. Emmanuel Yawe, sakataren yada labarai na kungiyar ne ya bayyana haka lokacin da yake tsokaci akan halin koma baya da yankin Arewa ke ciki, a wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Lahadin ƙarshen mako.

“Abin mamaki ne da baƙin yadda shugaban ya kasance tsohon soja amma ya kasa tabuka wani abin kirki akan harkar tsaro, kusan ma za a iya cewa gwamma jiya da yau”. Mr. Emmanuel ya bayyana yadda kungiyar ta ACF ke nuna damuwarta game da yadda kasar nan ke ciki, yana mai cewa, Arewa ta kasance cikin firgici, sannan babu zaman lafiya.

Yayin da aka tambaye shi irin damuwar da ACF ke ciki game da yawaitar tashe-tashen hankula a Arewa, Mr. Emmanuel ya ce: “Ka san muna matukar nuna damuwa game da yanayin tsaro a kasar fiye da kima yayin da mutumin da yake shugaban kasa ba kawai janar ne na yaki kadai ba, tsohon Shugaba ne na mulkin Soja a baya. “Ta yaya za ka ba da shawara ga gwamnatin da wani mutum ke jagoranta wanda yake da tsohon tarihin aikin tsaro?

“Wasu daga cikin mu da suka taka rawar gani a lokacin da ya hau kan karagar mulki a shekarar 2015 mun ji cewa abin da ke faruwa a halin yanzu ya kai abin kunya matuka.” ACF ta jima da gane Najeriya na cikin mummunan hali wanda sai dai ace Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here