Yadda Aka Gudanar Da Hawan Idin Karamar Sallah A Katsina.
An gudanar Hawan Idin karamar Sallah a jihar Katsina a ranar Litinin din bayan cika Azumi 30 na wannan shekara ta 1443H, hawan da aka shafe shekaru Uku cur ba a yi ba sakamakon annobar cutar Mashako ta ‘Coronavirus’ da kuma matsalar tsaro.
Tawagar Katsina City News ta shaida isowar Sarki da misalin karfe 9:00 na safiya a babban Masallacin Idi na jihar da ke kofar Guga, a kan hanyar zuwa Jibiya, inda kafin isowarsa aka fara gudanar da da jawabi da hudubobi wadda Malam Sirajo Lawal Liman ya gabatar, a yayin da Liman Malam Mustapha ya gabatar da huduba bayan ya jagorancin Sallar Idin.
Tun farko, Malam Sirajo ya fara share fage da yin tunatarwa a kan abubuwan da suka shafi bayar da Zakka, Zaman Lafiya, Tsoron Allah da kuma kyautatawa Makwafta.
Kafin ya sauka, bayan ya iso ya yi zamiya ga gwamnan jihar katsina a farfajiyar Kofar Soro da misalin karfe 1:00 na rana, a jawabinsa, Sarkin Katsina Alhaji Abdulmini Kabir Usman, ya yi wa al’umma jawabi a kan komawa ga Allah da kuma fitar da Zakka da kuma Tallafawa marar karfi.
A yayin gudanar da wannan hawa, sama da hakimai 40 ne suka yi hawa, a yayin da magaddai, dagatai, da sauran Makada da Mawaka ke raka su.
Tururuwar al’ummar jihar katsina ne sika fito kallon wannan Hawa wanda yake kamar bako a gare su, biyo bayan shekarun da aka dauka ba a yi hawan ba.
A tarihin hawan Sallah a Katsina, ana yin hawa biyu ne; Hawan Idi da Hawan Bariki. Hawan Idin da Gwamna ke yo takakkiya zuwa gidan sarki domin yin gaisuwar Sallah, a yayin da hawa na biyu wato hawan Bariki shi kuma ake gudanarwa kwana daya bayan Idi ( wanshekaren salla) inda sarki ke zuwa gidan gwamnatin jiha domin shi ma ya kai wa Gwamna gaisuwar Sallah.