AREWA MEDIA WRITERS.
Mujallar Zauren Marubuta Ta Kasa, Ta Karrama Kungiyar “Arewa Media Writers” Da Lambar Yabo Daga Kungiyar Arewa Media Writers A yau Lahadi “Mujallar Zauren Marubuta” ta kasa ta karrama kungiyar marubutan Arewa, a kafafen sadarwar zamani “Arewa Media Writers” reshen jahar Katsina da lambar yabo, a ya yin babban taron ta na kaddamar da harsashin fara buga Mujallar da zata rika fitowa a kowane karshen wata. A jawabin Shugaban gidan Mujallar Zaidu Ibrahim Barmo, yace sun karrama kungiyar ne duba da irin dinbim gudunmuwar da membobinta suke bayarwa a cikin al’umma tare da kare martabar Arewa ta hanyar rubuce rubuce musamman a kafafen sadarwar zamani. Haka zalika Mujallar ta sake karrama wasu daga cikin shugabannin kungiyar “Arewa Media Writers”, da suka wakilci uwar kungiyar a matakin kasa, wanda ya hada Babban mai tace hoto. SadiQ Ahmed Rabi’u da babban mataimaki na musamman a Ofishin Shugaban kungiyar na kasar Comr Abba Sani Pantami, wato El-faruq jakada. A Ya yin karramawar Shugaban kungiyar na “Arewa Media Writers” reshen jahar Katsina Comr Nura Siniya, tare da sauran masu rike da madafan iko da suka samu halartar taron sun godema Mujallar Zauren Marubuta tare da nuna farin cikin su bisa ga wannan karramawa da aka yi ma kungiyar. Taron ya gudana ne a babban dakin taro na (KVC) dake cikin birnin katsina. A karshe sun yi addu’ar Allah ya taimaki Mujallar akan aza harsashin fara fitar da rubuce rubucen su a duk karshen wata, don kawo cigaba ga al’umma. Comr Nura Siniya Chairman Arewa Media Writers Katsina State Chapter.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here