Muhimmin Saƙo Daga Ɗan Jarida Jaafar Zuwa Ga Masu Saka Kuɗinsu Wala -walar Intanet

Ina kira ga ‘yan uwa duk wanda yake da kudi a cikin tsarin wala-walar saka jari a internet ko ban-biyar-na-ba-ka-goma (Ponzi Scheme), to ya yi gaggawar cire kudinsa domin cuta ce kawai tsagoronta ba komai ba.

A gabanku wasu a baya su ka saka kudadensu a cikin wannan tsari amma ba su wanye lafiya ba, amma abin mamaki shi ne da zarar wani sabon tsari ya shigo, sai ka ga matasa su na tururuwa su na shiga, uwar dashi ta tarkata kudin mutane ta shiga, wata kuma ta dauki kudin marayu ta shiga, wani kuma ya kwashe jarinsa kaf ya shiga.

Ya kamata a ce rushewar MMM da INSME da INKSNATION da Swiss Golden Investment da MGB Global Market da BOONBUY da sauransu ya zama izna ga mutanenmu. A yanzu haka na ji labari irin su Uwork da Mybonus da GetApp su na nan su na shan sharafinsu.

Ga jerin wasu kamfanonin wala-wala da hukumar tantance kamfanonin hannun jari ta kasa (SEC) ta fitar a wattanin baya:

Loom Nigeria Money
Box Value Trading Company Ltd
Now-Now Alert
Flip Cash Investment
Result Investment Nigeria Limited
Helping Hand and Investment
No Failure Development and Empowerment Nigeria Ltd.
MBA Forex and Investment Ltd
Federate Investors and Trading Company
Jamalife Helpers Global Ltd
Flexus Global Solutions and Investment Ltd
United Capital Investment Company Limited.
Daga jafar jafar..mawallafin jaridar Daily Nigeria

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here