Advert
Home Sashen Hausa MUHAWARA; Ra ayina akan ginin tsohuwar ma aikatar watsa labarai .......Daga wani babban...

MUHAWARA; Ra ayina akan ginin tsohuwar ma aikatar watsa labarai …….Daga wani babban sakataren  jahar katsina 

 

@ katsina city news

Ina ganin lokaci yayi da kowa zai fadi raayin shi akan wannan lamari.

Ni a gani na, zai fi kyau idan gwamnati ta zauna ta tsara ma tsohon wurin nan zane mai kyau don a gyara shi yayi daidai da, zamani kuma ayi providing library na zamani mai facilities na elibrary da komai. Yana da kyau ya zama wannan cibiya tana zaune a nan inda take sbd yara ne yan makarantar primary, secondary da university ake sa ran zasu zo suyi karatu da bincike a wannan wuri. Zai fi kwanciyar hankali ga kowa ace wuri irin wannan yana cikin tsakiyar gari don tabbatar da tsaro da sa idon hukuma da na abota muamullar karatu da bincike. A samu isasshen wurin aje ababen hawa da hutawar mai karatu a wurin. Idan ya zama dole ma babu damuwa a hada hadda tsohuwar finance a cikin wannan gyaran sbd muhimmacinsa ga al’ummar yanzu da ta bayan mu.

Shi kuwa green house kasuwa ce wadda dama an fi zaton manyan mutane ba yara ba ke hudda a cikinta kuma duk mai dalilin zuwa kasuwa ko ina take zai bi ta yaje, hasali ma dai kasuwa tana bukatar fili don fadadawar yau da gobe kuma tana bukatar kyakkyawan tsari don jamian tsaro da kiyaye gobara da wadatar wuraren biyan bukatu da issasun hanyoyin shige da fice da sauran su, sbd haka a fidda kasuwa waje, a ajiye dakin karatu a gari yafi kyawon tsari da biyan bukatar al’umma a ra’ayi na

Marubucin nan ya rubuta kuma ya bukaci a sakaya sunan shi.

@ katsina city news

Www.katsinacitynews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: