Muhammad Salah: Dole Ne A Kawo Karshen Keta Alfarmar Masallacin Quds Da Kisan Falastinawa

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya Muhammad Salah ya yi kira da a kawo karshen keta alfarmar masallacin Quds mai alfarma da kuma kisan da ake yi wa Falastinawa.

Muhammad Salah Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa fa Liverpool ya bi sahun da dama daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, wadanda suke kira ga kasashen duniya da su takawa Isra’ila burki kan kisan kiyashin da take yi wa fararen hula a Falastinu.

Muhammad Salah ya ce, wajibi ne kan al’ummomin duniya da gwamnatoci da su gagaguta daukar matakin kawo karshen wannan zubar da jinni na bayin Allah da ake yi a Falastinu.

Haka nan kuma Salah ya kirayi Firayi ministan kasar Burtaniya Boris Johnson, da ya yi amfani da karfin fada aji da yake da shi wajen ganin an kawo karshen wannan kisan gilla na Isra’ila a yankunan Falastinawa

Kafin haka, wasu da dama daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na duniya sun fitar da bayanai makamantan hakan, daga ciki kuwa da abokinsa da suke buga wasa a Liverpool Sadio Mane dan kasar Senegal, wanda shi ma ya yi Allawaai da kisan gillar da Isra’ila ke yi kan musulmin Falastinu.

Su a nasu bangaren ‘yan wasa irin su Paul Pogba da ke buga wasa a Manchester United, Franck Ribery da ke wasa a Fiorentina, Ousmane Dembélé da ke wasa a Barcelona, da makamantansu da dama, duk sun fitar da bayanai na yin kira da a kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila take yi kan al’ummar Falastinu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here