Advert
Home Sashen Hausa Muddun Gwamnatin da zata zo nan gaba batafi tamu ba to bamuci...

Muddun Gwamnatin da zata zo nan gaba batafi tamu ba to bamuci gaba ba -Aminu Masari-

Muddin Gwamnatin Da Za Ta Zo Nan Gaba, Ba Tafi Ta Aminu Bello Masari Ba, Ta Ba Za Mu Ci Gaba Ba, Cewar Gwamna Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa duk gwamnatin da za ta zo a 2023 ba tafi ta gwamnatina ba, to jihar Katsina ba za ta ci gaba ba, saboda cigabanmu shi ne a kawo wadanda za su yi fiye da abinda muka yi, shi ne jihar Katsina za ta ci gaba.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ci gaba da shirye-shiryen zaɓen Shugabannin jam’iyyar APC a matakin jiha da za’a yi a ranar Asabar mai zuwa idan Allah ya kaimu. Wanda ya gudana a yau Alhamis a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Masari ya ci gaba da cewa ni nan ba so nike ace ba wanda ya fi ni ba, fatana ni ke a lokacin da na bar wannan kujera, ko da abun alheri daya a gwada a ce ni na asassa shi, wata rana a ce ni na kawo shi, shikenan na samu biyan buƙata.

Gwamna Masari ya kara da cewa jihar Katsina ita ce a gabanmu, saboda mu dukkan mu za mu mutu mu bar jihar Katsina. Ni ina fatan jihar Katsina ta yi nasara a ko da yaushe na kasance ina da guddumuwar da na ba da. Abinda za’a yi nasarar APC ce ba ta wani mutum guda ba, mu nan dukkan mu jam’iyyar APC ta biya bashin dake kanta, mu ne za mu biyata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: