“Mu Ne Matsalar Kasarmu” – Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum Bauchi.

“…Malam ka dubi yadda kasarmu ta lalace. Idan wani abu ya faru, sai a je a nemo wani mai fashin baki a gidan radio ya zo ya yi fashin baki. Sai ka ga inda matsalar kasar ta yi daban; inda fashin bakinsa ya yi daban. Shi ma wanda yake fashin bakin, yana bukatar a yi masa fashin baki.

Ai ka kalli kasar ka kalli makomar kasar, duk wanda zai kalli Kasarmu da hangen nesa, ya kalli abin da zai je ya dawo; ya san abubuwa a kasar sun lalace. Matsalar Kasarmu shi ne hanyar cin abincin kasar, (matsalar kasar shi ne hanyar samun kudin kasar) ka gane?

(1) Lalacewar Ilimi shi ne hanyar samun kudin wadansu. Lalacewar makarantun Gwamnati shi ne hanyar samun makurantun da ba na Gwamnati ba. Idan makarantun Gwamnati suka gyaru, to makarantu ‘private’ ba za su samu mutane ba. Kuma Malam wallahi wadannan ma su makarantun ‘private’ babu wanda zai sha kansu; ba Kwamishina ba ko Ministan Ilimi ba zai sha gaban su ba. Wannan matsalar ta ilimi, ita ce hanyar cin abincinsu.

(2) Matsalar Man fetur ita ce hanyar samun kudin masu harkar mai. Saboda wanda ya ke sana’ar mai idan aka samu wahalar mai abin da zai samu a sati biyu, in za a je a latsa ne a gidan mai a samu, sai ya shekara bai samu wannan kudin ba. Don haka matsalar mai ita ce hanyar cin abincinsa.

(3) Matsalar wuta ita ce hanyar samun kudin wasu. Wadannan masu harkar man fetur, Wallahi ba Ministan Man fetur ba ko shugaban Kasa sai ya yi da gaske zai iya shan gabansu.

(4) Matsalar tsaro shi ne hanyar samun kudin wasu masu tsaron idan aka zauna lafiya ba za su samu kudin da suke so ba. Saboda haka matsalar tsaro shi ne hanyar samun kudinsu. Wannan shi ne gaskiya. Saboda haka matsalar mu ita ce hanyar samun kudinmu, saboda haka matsalar ba za ta kare ba.

(5) Yanzu ka san iyakan kudin da ake samu ga matsalar Cronavirus? Wadansu sanadiyar hanyar arzikinsu shi ne hanyar Cronavirus. To idan ka dubi wannan ita ce matsalar kasarmu, yaushe ne Kasar za ta gyaru?

Mu da ya kamata mu hada kudi da karfi a kan gyaran Kasar, sai ya zama matsalar kasar ita ce hanyar neman kudinmu. Sai ka gayamin, yaushe ne kasar za ta gyaru? Saboda haka dole sai mun ji tsoron Allah, sai mun dubi ‘ya’yanmu da jikokinmu, sai mun dubi addininmu.

Idan ka ce abincin da za ka ci gobe, yau ko jibi shi ne matsalar ka, to gobe za a ritsa da ‘ya’yanka da jikokinka yau ko jibi. Saboda haka, mu ne matsalar kasar mu, kar ka dauka wani ne matsalar. Saboda haka kowa ya gyara. Jami’an tsaro su ji tsoron Allah su gyra, masu harkar ilimi su ji tsoron Allah su gyara, harkar wuta, harkar kasuwa, harkar ofishi duk su ji tsoron Allah su gyara.

Yanzu fa masu masara suna nan sun tara jibgi-jibgi jira suke ta fara yankewa. Wani yana nan ya siyo masara buhu a kan farashin dubu bakwai (N7000) wani dubu takwas (N8000), yana nan ya 6oye yana jira a shiga matsalar rashin abinci sai ya fitar ya dinga sayarwa bubu daya dubu goma sha bakwai (N17000). Shi a tsadar abinci a Kasarsa shi ne hanyar samun kudinsa. Saboda haka matsalar kasar ita ce hanyar cin abincin ‘yan kasar, waye zai yarda hanyar abincinsa ta yanke?

To inda za ka gane matsalar da gangan ne, za ka samu Malami yana karantarwa a makarantar gwamnati ana bashi N50,000 amma bai wuce ya je sau uku ko biyu a rana ba, amma sai ka samu ana ba shi N15000 a makarantar ‘private’ amma bai isa ya tsallake rana daya bai je ba. Kuma fa dubu goma sha biyar ake ba shi, ga inda ake bashi dubu Hamshin. Kuma fa Malaman da ke karantar da Makarantun Gwamnati su ne suke karantarwa a private, kowa ya san ba Aljannu ba ne suke karantarwa a private ba. Me ya sa Makarantun private ake cin jarrabawa bayan duk Malamai daya ne suke karantarwa? Kawai da gangan ne ake yin wannan domin a lalata makarantun gwamnati. Ka duba kudin da yake samu a makarantun gwamnati sun fi na private, amma abin kunya aikin da yake yi a private ya ninka wanda yake yi a makarantun gwamnati. Shi yana cikin masu kashe kasa ko baya ciki?

Saboda haka, matsalar kasarmu, mu ne! Ka daina nuna wani ka ce su wane ne, har da kai! Matsalar mu ne, Matsalar mu ne!”

Allah Ya sa mu gyara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here