Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa Gwamnatin Jiha, hadin guiwa da jami’an tsaro da kuma masu ruwa da tsaki kan harkar tsaron, suna kan wani shiri na musamman wanda zai samar da yanayin da manoma za su noma gonakinsu lami lafiya in sha Allah.

Shirin wanda ya shafi dukkan kananan hukumomin da suke fama da hare haren ‘yan ta’adda, zai inganta harkar tsaron, kuma da yardar Allah manoma za suyi harkar su cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labaru a Ofishin shi dake fadar Gwamnatin Jiha.

Da ya juya ta bangaren ‘yan kasuwar Katsina da ibtila’in gobara ya afkamawa kuwa, ya bayyana cewa tuni Gwamnatin Jiha ta ware kudin da za a tallafa masu, tuni kuma kwamitin da aka kafa don hakan, yana kan aiki ka’in da na’in don ganin an tallafa masun gami da tallafin da aka samu daga hannayen wasu bayin Allah. Ya kuma kara tabbatar da cewa duk wanda ya rasa rumfa zai sami rumfa. Haka kuma duk mai son ya gina tashi da kan shi to dole yabi taswira da ka’idojin da aka gindaya ma aikin.

Haka kuma, Gwamnati na sane da kokarin da wasu ke tayi na ganin sun haddasa husuma cikin wannan al’amari don biyan wasu bukatun su na kan su, ana kira gare su da subi hanyar da ta dace wajen gabatar da duk koken da suke dashi.

Da aka tabo maganar zaben kananan hukumomi kuwa, Gwamnan ya tabbatar da cewa tuni shirye shirye sun yi nisa, domin an kammala a kalla kashi Saba’in cikin Dari (70%), babban abinda ya rage shi ne gurza takardar kada kuri’a wanda kuma sai an sa ranar zabe ake yin wannan. Ya kuma bada hasken cewa da zarar kotuna suka dawo aiki, Gwamnati za ta amso cikakkun bayanan dake kumshe cikin hukuncin da babbar kotu ta yanke kan rushe kananan hukumomi da akayi. Ya kara da cewa tun kafin babbar kotun ta yanke hukuncin suka biya kaso da dama na kudaden ga tsaffin shuwagabannin kananan hukumomin da mukarraban su.

-AbdulHadi Ahmad Bawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here