MOTSIN SIYASA A KATSINA;31 GA JANAIRU 2021

muazu hassan
@ katsina city news
A ranar 31/1/2021 Rana daya kusan lokaci daya aka fara wani motsin siyasa a jahar katsina Wanda ya karade da ya shafi duk fadin jahar don buga kugen amsar mulki a 2023.
A ranar wasu halastattun yan jam iyyar APC sukayi wani taro a Kano karkashin wata kungiya mai suna APC pressure group. Manufarsu ta bayyane ayi adalci da dimorakadiyya a cikin jam iyyar APC.manufarsu ta boye amsar mulki a 2023.
A dai garin Kano dai dai lokacin, APC pressure group sun taru a prince hotel. Su kuma tsaffin kantomomin jam iyyar APC karkashin jagorancin Abubakar soja tsanni, sun taru a Rk hotel dake Kano.
A taron sun tattauna da jaddada goyon bayansu ga gwamnan katsina da shugaban jam iyyar APC na jaha Alhaji shitu s shittu da Kira a fito ayi katin jam iyya.wannan ce manufarsu ta bayyane ta boye kuma 2023.
A Dai dai lokacin a garin Kaduna jahar Kaduna.sanata abu Ibrahim yana taro da wai masu ruwa da tsaki na jam iyyar dake shiyyar funtua. Babu takamaiman bayanin manufar taron da zalla yaran abu Ibrahim ne.amma kowa ya San dundufar 2023 ce.
A katsina ma wasu kungiyoyin matasa karkashin jagorancin matashin nan da yace wai ya taka daga katsina wai yaje har Kano wai kasa wai don taya ganduje murna. Nura Ali batsari shima ya hada wasu kungiyoyin matasa suka ce sun fito ne don nuna goyon bayansu ba arch Ahmad dangiwa.cikin hotunan dake yawo harda na tsoho dan shekaru sama da Saba in a matsayin matashi.maganar itace 2023
A ranar hamshakin attajiran nan na katsina yaje gaisuwa da jaje ga Dikko Radda akan Rasuwar Dan uwanshi.da sako Dan uwanshi daga hannun masu garkuwa da mutane .ziyarar da ake ganin kulla zumuncin siyasar 2023 ce.
A daidai lokacin wasu matasa na bisa wani bene suna tattauna ya zasu fara tallata mataimakin gwamnan katsina gwarzonsu a shafukan yanar gizo? Kodayake an tashi baram bara.akan wa zai shugabanci tafiyar. Daga baya sun dai dai ta.2023 ce
A ranar wasu matasa daga funtua suka yanke shawarar su zo katsina kawo ma sakataren gwamnatin katsina ziyarar nuna goyon baya in har ya fito takara a 2023. Matasan sun gayyaci katsina city news ta rufa masu baya don dauko rahoton
Wannan itace ranar 31 ga JANAIRU 2021 a jahar katsina. Am fara kenan
________________________________________________
Katsina city news na a bisa yanar gizo www.katsinacitynews.com da sauran shafukan sada zumunta. Yan uwanta sune jaridar taskar labarai dake www.taskarlabarai.com da kuma the links news dake www.thelinksnews.com. duk sako ga 07043777779.email.katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here