Advert
Home Sashen Hausa Mohamed Bazoum ne kan gaba a sakamakon zaɓen Jamhuriyyar Nijar

Mohamed Bazoum ne kan gaba a sakamakon zaɓen Jamhuriyyar Nijar

Mohamed Bazoum ne kan gaba a sakamakon zaɓen Jamhuriyyar Nijar

@MOHAMED BAZOUM

Sakamakon farko-farko na zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyyar Nijar na nuna cewa ɗan takarar jam’iyya mai ta PNDS Tarayya Bazoum Mohammed ne yake kan gaba da ƙuri’u sama da 400,000.

Sai mai bi masa Alhaji Mahamman Osmane na jam’iyyar RDR Canji yake da ƙuri’u yake da ƙuri’u sama da 140,000.

Hukumar zaɓen ƙasar CENI ce ta bayyana yawan ƙuri’un da kowane ɗan takara ya samu a yayin da ta bayyana sakamakon gundumomi 77 daga cikin 266 na zaɓen shugaban ƙasar.

Hakazalika CENI ta sanar da sakamakon gundumomi 55 da cikin 266 ɗin na ƴan majalisar dokoki.

Sai dai jam’iyyun ƙawancen adawa na Cap 2021 ya fitar da wata sanarwa yana zargin jam’iyyar PNDS Tarraya da tafka maguɗi ta hanyar amfani da kuɗi wajen sayen masu zaɓe da ma fashin akwatin zaɓe.

Ƙawancen ya kuma bayana cewa ba zai taɓa amincewa da wani sakamako ba da bai fito daga akwatunan zaɓe ba.

Sai dai da yake mayar da martani, Alhaji Daoui Ahmed shugaban matasa na jam’iyyar PNDS Tarraya ya yi watsi da zargin nasu inda ya shaida wa wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou cewa hakan bai zo musu da mamaki ba.

PNDS Tarayya ta ce ta a yanzu hankalinta kwance yake ta yi haƙuri har hukumar zaɓe ta kammala faɗar sakamako gaba ɗaya.

Alhaji Ahmed ya ce ba sa kokonton cin zaɓe don jam’iyyarsa ta yi wa al’ummar Nijar aiki tsawon shekara 10, kuma a tsawo wannan lokaci sun shafe shi suna neman goyon bayan al’ummar ƙasar.

A yankin Damagaram ma aikin ci gaba da tattara sakamakon ake yi inda aka karɓi na shiyyoyi 38 daga cikin 45 da ake da su a jihar.

Sai dai ko bayan an kammala tattara sakamaon daga Damagaram da sauran jihohi to miƙa shi zuwa Yamai a kan ɗauki lokaci, kamar yadda wakilin BBC Ibrahim Isa ya faɗa.

“Ko sakamakon yankin da ɗan takarar jam’iyya mai mulki ya fito ma bai iso ba har yanzu, don haka akwai sauran jira a gaba,” in ji Ibrahim.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da manyan zaɓukan Jamhuriyyar Nijar ɗin inda aka fara kaɗa ƙuri’a da ƙarfe 08:00 agogon Nijar a rufe da ƙarfe 07:00 na dare.

Kusan mutum fiye da miliyan bakwai ne suka kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen har da ɗumbin matasa da suka kai shekarun yin zaɓe.

‘Yan takara 30 ne suka fafata da juna don karɓar ragamar mulki daga Shugaba Mahamadou Issoufou, bayan ƙarewar wa’adinsa biyu tsawon shekara goma.

Zaɓen shi ne irinsa na farko da wani zaɓaɓɓen shugaban ƙasa zai miƙa mulki cikin ruwan sanyi ga wani takwaransa da za a zaɓa.

Kuma ko ma wane ne zai zamo sabon shugaban Jamhuriyar Nijar a Lahadin nan, zai fuskanci ƙalubala iri daban-daban ciki har da taɓarɓarewar tsaro da cin hanci da rashawa da kuma talauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?….Siyasar zaben 2023

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM'IYYAR APC? . ..Siyasar Zaben 2023 Mu'azu Hassan @ Katsina City News Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan...

Bikin bada sandar girma a Masarautar Rano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya Jagoranci mika sandar Girma ga Mai Martaba Sarkin Rano, Amb. Alh. Kabiru Muhammad Inuwa Autan...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Nada Amina Muhammad Daga Jihar Gomben Najeriya Karo Na Biyu

Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa. An sake...

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021 DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya...
%d bloggers like this: