Minista a Ma’aikatar Ciniki da Zuba Jari, Ambasada Maryam Katagum ta yanke jiki ta fadi tana tsaka da wata ziyarar aiki a Jihar Bauchi.

Rahotanni sun ce nan take aka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU-TH) domin samun kulawar gaggawa.

Ministar dai ta je Bauchi ne domin kaddamar da wani shirin tallafawa jama’a a daya daga cikin manyan kantina a Bauchi, amma kwatsam sai ta yanke jiki ta fadi a daidai lokacin da take kokarin gabatar da jawabi.

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad da Mataimakinsa, Sanata Baba Tela da sauran manyan mukarraban gwamnati na wurin a lkocin da lamarin ya faru.

Wani ganau a inda lamarin ya faru ya shaida wa wakilinmu cewa Minista Maryam ta fadi ne a daidai lokacin da ta mike don gabatar da jawabi.

“Kawai gani muka yi ta dafe kanta ta fadi a kasa, amma an samu an garzaya da ita zuwa asibiti cikin gaggawa,” inji shi.

Wani babban jami’in gwamnatin Jihar ya shaidawa ’yan jarida cewa da zarar ta sami sauki za a mayar da ita Abuja domin ta ci gaba da samun kulawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here