Ministan Noma Sabo Nanono Mai Shekaru 74 Ya Auri Tsaleliyar Budurwa ‘Ƴar Shekara 18

Daga Jaridar Daily Nigerian

Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono, ya auri yarinya ‘yar shekaru 18 da ta bar makaranta a cikin wani bikin sirri, kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta bayar da rahoto da karfin iko.

Minista Nanono, mai shekara 74, ya daura auren tare da kyakkyawar matar a wani bikin sirrin da ya samu halartar wakilai uku na ango da ke garin Jere na jihar Kaduna.

“Ministan ya sanya mutane uku ne kawai kuma ya gargade su game da bayyana dalla-dalla game da auren ga mutane,” in ji wata majiya daga dangin da ta fi son a sakaya sunanta.

DAILY NIGERIAN ta samu labarin cewa amaryar, wanda kawai aka ambata da Rakiya, tuni ta sauka a gidan ministan a Tamandu Close da ke Kano.

Duk da cewa dangin ministan sun nuna adawa ga bikin, amma majiyoyi sun ce Minista Nanono ya dage kan ya auri yarinyar duk da bambancin shekaru sama da 50 da haihuwa.

“Ministan yana hauka da soyayya. Ya bayyana ba za a iya dakatar da shi ba.” In ji majiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here