Ministan mai a Najeriya ya nemi afuwa kan ƙarin kuɗin fetur

Timipre Sylva

Ƙaramin ministan man fetur na Najeriya ya nemi afuwar ‘yan ƙasar kan “wahalhalun da suka shiga” bayan ɓullar labarin ƙarin kuɗin man a safiyar yau Juma’a, wanda ya bayyana da “abin baƙin ciki”.

Da sanyin safiyar Juma’a ne hukumar kula da farashin fetur (PPRA) ta mayar da litar man zuwa naira 212 daga 163, amma daga baya ta ce yadda ake cinikin man a kasuwa kawai ta bayyana ba ƙari a kan yadda talakawa ke saya ba.

Timipre Sylva ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, yana mai cewa daga shi har Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne babban ministan man fetur, babu wanda ya amince da ƙarin zuwa naira 212 kan kowace lita.

Ya ƙara da cewa duk da bai san daga inda aka samu labarin ba, “ina so na tabbatar muku cewa ƙarya ce zallanta”.

Lamarin ya jawo ɓacin rai daga ‘yan Najeriya, inda suka riƙa sukar gwamnatin Shugaba Buhari, wadda ta haƙiƙance cewa ba za ta ƙara kuɗin man ba a cikin watan Maris.

PPRA ta goge bayanan farko da ta wallafa a shafinta na intanet game da ƙarin kuɗin man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here