(004)
Ministan Abuja Ya Hana Gudanar da Sallar Idi A
Filin Idi na #Kasa
________
A wani bangare na kokarin shawo kan barkewar
cutar COVID-19, Ministan Babban Birnin Tarayya
(FCT), Malam Muhammad Bello, ya hana yin
sallar idi a filin sallar Idi na kasa da ke kan
babbar hanyar Umaru Musa Yar’Adua.
A cewar wata sanarwa daga Babban Sakataren
yada labarai na Ministan, Mista Anthony
Ogunleye, an yanke shawarar ne a taron FCTA
da kuma wata tawaga daga kungiyar Limaman
Abuja (FCT League of Imams Initiative).
Ogunleye ya ce tawagar a karkashin jagorancin
Shugabanta, Imam (Dr) Tajudeen M.B Adigun,
sun sadu da Bello ne domin tattaunawa kan
hanyoyin da za a bi domin gudanar da sallar idi
domin bukukuwan Idin Karamar Sallah mai zuwa
“An umarci dukkan masu ibada da gudanar da
sallar idi a waje a cikin harabar masallatan
Juma’a na unguwanninsu. A iyakance adadin
masu sallah a cikin harabar masallaci zuwa ƙasa
da kashi 50% na yawan mutanen da yake
dauka.
“An shawarci hukumomin addinai da su
daidaita yawan shigowar mutane da kuma fita
daga wuraren ibada. A kiyaye duk ka’idoji da ba
su shafi magani ba na rufe fuska, nisantar jiki
da wanke hannu.
“Duk sauran bukukuwan idi da aiyuka ya kamata
a yi su a cikin gidaje kamar yadda duk wuraren
shakatawa na jama’a da wuraren nishadi za a
rufe,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here