Ministan Abuja Ya Bada Umarnin Cafke Masu Warwason Kayan Tallafin Korona

Har yanzu fusatattun matasa suna ci gaba da balle dakunan ajiyar kayan tallafin korona da gidajen wasu ‘yan siyasa. A yau Litinin ma wasu matasan sun balle wani babban dakin ajiyar kayan abinci da ke Gwagwalada, Abuja
Ministan Babban birnin tarayya Abuja, ya bukaci jami’an ‘yan sanda su kama wadanda suka warwason kayan cikin dakin ajiyar tare da gurfanar dasu a gaba kuliya. Ministan babban birnn tarayya, Abuja, Malam Muhammad Bello, ya bayar da wannan umarnin ne, sakamakon barnar da suka yi na balle babban dakin kayan abinci da ke garin Gwagwalada tare da gurfanar da su a gaban kotu.
An yi wannan warwason a jihohin Filato, Kaduna, Adamawa, Kogi, Legas Ribas da ma Jihar Kwara, zuwa yanzu hukumomi da sun fara farautar masu warwason, inda a garin Jos na jihar Filato tuni jami’ai suka cafke kusan mutum 200, wadanda suka ce in Allah ya nuna mana gobe Talata za su gurfanar da su a gaban kotu.