Advert
Home Sashen Hausa "MILIYAN HAMSIN DA NASAYI  FOM ƊIN TAKARA DAI-DAI SUKE DA GWANGWANIN GYAƊA...

“MILIYAN HAMSIN DA NASAYI  FOM ƊIN TAKARA DAI-DAI SUKE DA GWANGWANIN GYAƊA A WAJENA”……..UMARU TATA

“MILIYAN HAMSIN DA NASAYI  FOM ƊIN TAKARA DAI-DAI SUKE DA GWANGWANIN GYAƊA A WAJENA”……..UMARU TATA

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Umar Abdullahi Tsauri TATA, wanda akewa inkiya da Mai Dubu-dubu, ya kaddamar da takarar sa ta neman zama Gwamnan jihar Katsina a kakar zaɓe mai kamawa, ranar juma’a a garin Dutsin-ma.

Tata ya fara gabatar wa mahaifarsa ta Dutsin-ma da Jam’iyyar sa ta APC a ƙaramar Hukumar sa, kansa a matsayin mai neman takarar Kujerar Gwamnan jihar Katsina, inda ya bayyana a gaban Ɗinbin Masoyan sa, tun daga gidansu, ya ɗare bisa Doki, inda ya zagaya garin Dutsin-ma, yana nuna kansa ga al’umar Dutsin-ma, har zuwa Offishin Jam’iyyar APC na ƙaramar Hukumar ta Dutsin-ma a yayin da al’uma Maza da Mata suka tarbeshi da kiɗa gami da guɗa, Busar ƙaho ga Matasa, har zuwa cikin Ofishin inda ya rattaba hannu akan takardar shaidar tabbacin Fitowa a cikin maneman Kujerar ta Gwamna.

Bayan nan Tata ya fito a farfajiya domin yin takaitaccen jawabi ga Masoyan sa, inda kafin Umar Tata ya fara jawabin saida Shugaban Jam’iyyar APC na ƙaramar Hukumar ta Dutsin-ma ya gabatar da jawabi na fatan Alheri da addu’a inda ya rokama TATA, nasara har  zuwa Kujerar Shugaban ƙasa.

Tata ya gabatar da jawabi mai Falle biyu ga ɗimbin magoya bayan sa da suka taru a wajen, gami da ƙudirorinsa. A ƙarshe ya isar da saƙo inda yace.

“Ni inada ƙudiri guda biyu, kuma idan Allah ya tabbatar mani da Kujerar Gwamnan Katsina, zani Aiwatar da su. Na farko tsaro na biyu gina Sabuwar jihar Katsina.”

Umaru Tata ya faɗi hanyoyin da zai bi domin cimma ƙudirorinsa, inda ya ce zai samar da Ma’aikatar tsaro, wanda yin haka zai kawo ƙarshen ta’addanci a jihar. Sana zai gina jihar Katsina ta hanyar samarda ababen more rayuwa da bin diddiƙi don ganowa da zaƙulo duk wasu waɗanda Ibtila’in ‘yan bindiga ya shafa domin gina masu Sabuwar rayuwa.

A saƙon sa ga Jam’iyyar APC kuma Tata ya bayyana jin dadin sa ƙwarai da gaske game da karamci da yace ammasa wanda bai taɓa samunsa a Jam’iyyar PDP ba injishi, inda ya bayyana misalai daban-daban har ga shugaban Jam’iyyar da ya masa fatan zama Shugaban ƙasa. Ya ƙara da cewa; “Ina nan Jam’iyyar APC idan Allah ya bani Gwamna zanyi iya kokarina domin gina jihata da al’umata, idan kuma Allah bai bani ba, zan ci gaba da taimakawa Jam’iyya ta. Wasu suna cewa Tata bashi da ƙudin siyen Fom, Naira miliyan Hamsin, to ku sani ni Tata waɗannan kuɗin na sayen Fom kamar Gwangwanin gyada suke da zan saya inci in watsar da ɓawon ni a wajena.” Inji Tata.

Da yake magana akan tsakanin shi da Gwamnatin Katsina da Aminu Masari yace: Shi a iya saninsa Babu Abinda Masari ya taba yi masa na ba daidai ba, ko wani saɓani, tsakaninsa da Gwamna sai alheri saboda Masari yayimasa abinda Ibrahim Shema bai yi masa ba duk da sun fito daga ƙaramar hukuma guda.

Umar Abdullahi Tsauri TATA tsohon Ɗan gwagwarmayar Siyasa ne a jihar Katsina da ya taɓa fitowa takarar Gwamna har sau uku a jam’iyyu mabanbanta, Ya fito a Jam’iyyar PDP, APGA  da APC. Shine ya ɓullo da wani tsari na haɗa Matasa maza da mata Aure, da yi masu kayan ɗaki a duk faɗin jihar Katsina, da bada jari ga Mata da Marayu.
A shekara ta dubu biyu da sha hudu Umaru Tata ya Ɓullo da wani tsarin Taimakon Al’uma ta hanyar Cankar ƙuri’a abinda ka ɗauko Allah ya ci da kai za’a baka, wasu sunci Kujerar Makka wasu sunci Motar hawa, wasu sun samu Motar NAPEP, kekunan ɗinki, da na saƙa, wasu kurar Ruwa da kayan Noma.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

MATSALOLIN TSARO: Gwamnatin Zamfara tabawa duk dan jiharta damar Mallakar Bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Bai Wa Ƴan Jihar Damar Mallakar Bindiga don kare kansu daga harin ƴan bindiga Gwamnatin Zamfara da ke arewa maso yammacin...

NIMET Installs Message Dissemination Platforms At Abuja, Kaduna, P/H Airports #Positivefacts

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02SkXT7vgAdTkuHz5gW6EaSFt3qZoc4hVMtBMXRMw6SzFv1da5ujPAsEmWyd535tYgl/ Nigerian Meteorological Agency (NiMET) has procured and installed seven automatic message dissemination platforms at Abuja, Kano, Lagos, Maiduguri, Kaduna, Enugu, and Port Harcourt airports. The...

FISHERIES PROJECT CREATES JOBS TO OVER TEN MILLION NIGERIAN #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid0Gc6v3B4e1KT8u7qGbmcMUofbzSaejnB1PTcdjHrBSUaUtQA28bQNeQ3qgLAnhBfzl/The federal government under the leadership of president Muhammadu Buhari, GCFR, has create over ten million jobs to Nigerian through fisheries project, the honourable minister...

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje….. Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina.

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje..... Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina. Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina...

Yunƙurin Ficewar Sanatoci 20 Daga APC: Ku Nemawa Kanku Mafita Tun Kafin Wuri Ya Kure Maku – Hon. Ɗanlami Kurfi

Kamar yadda rahotanni ke cewa akwai kusan Sanatoci 20 na jam'iyyar APC da ke kokarin ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai da suka ƙi...
%d bloggers like this: