MENENE KUDURIN HESDIN A KAN MATSALA TA TSARO A DUTSINMA DA KUMA MAKWABTAN TA?

MENENE KUDURIN HESDIN A KAN MATSALA TA TSARO A DUTSINMA DA KUMA MAKWABTAN TA?

Daga Umar Tata

A yan kwanakin nan rubuce rubuce sunyi yawa a kan wannan kungiya da aka kafa a garin Dutsinma domin nema da bada tallafi ga matsalar tsaro ga karamar Dutsinma da kuma makwabtan ta inda har wasu suke sakin irin takardun da na rubuta ma wasu ofisoshin gwamnati na kasa domin neman tallafi a madadin ita kungiyar bisa umurnin yan kungiyar.

Da farko dai ina son jama’a su sani ita wannan kungiya an kafa ta ne domin Dutsinma kacokam amman da ta fara aiki sai ta fahimci cewa kare Dutsinma ba tare da bada gudummuwa ba, a inda zata iya, in har wadatar ta samu, to taimaka ma makwabta na sauran kananan hukumomi na Katsina zone shima taimako ne ga tsaron Dutsinma. Yau in har Dutsinma na zaune lafia amman babu zaman lafia a Safana ko Kurfi ko Danmusa ko Batsari to wannan yana iya shafar Dutsinma ko da kuwa ta yan gudun hijira ne.

Aikin da wannan kungiya ta saka a gaba kafin wannan cece kucen ya taso sune:

1) gyara motoci guda hudu (4) daga cikin biyar na yan sanda wadanda tsaye suke wata da watanni basu aiki sai kuma gyara ita gudar kwara daya tal wacce ke motsi amman tana tattare da matsaloli.
2) sayen sababbin motoci hilux hilux ga yan sanda da kuma Civil defence wadanda su ko keke basu dashi don aiki.
3) sayen baburan hawa domin aiki ga jami’an tsaro.
4) sayen motoci da babura ga kungiyar yan banga domin aikin su kasancewar tunda suke aiki basu da gatan da wani zai basu babur ko mota domin aikin su.
5) sayen kayan aiki wadanda doka ta yarda dasu kamar makamai, uniform, boots, usir usir, da walkie talkie ga mutum 575 masu aikin banga a karamar hukumar Dutsinma.
5) kungiya ta rubuta ma Mai Girma Gwamnan Katsina takarda ta neman filaye guda ukku domin:
a) gina Area Command na DSS ga tsohuwar Dutsinma local government kamar yanda ke da akwai shi a Funtua da Malumfashi amman babu a Dutsinma saboda rashin fili.
b) gina office na yan banga mai kayatarwa domin karrama su da basu dama da walwalar aiki bisa sanin muhimmacin aikin su ga al’umma.
c) gina babban dakin taro (town hall) da wurin ganawa da yin bukukuwa, swimming pool, wurin wasan kwallon kafa ta awa awa da sauran wasanni da kuma lambu wurin wasan yara watau children’s park da za a saka shillo, motocin wasa da saura kaya kala kala na kananan yara domin samun kudin shigar da kashi hamsin na kudin zasu rinka tafiya ne ga yan banga domin tafiyar da aikin su kamar sayen man mota da babura, service da dai sauran su. Tuni kungiya ta bada aikin zanen wannan ginin ga maaikatan gini da zane zane watau Architects.
6) kungiya ta yi shirin aje kudi a gidajen mai na Dutsinma duk wata wata domin motocin jami’an tsaro na yan sanda, sojoji da kuma Civil defence su rinka shan mai kyauta domin aikin su don gudun kar rashin mai ya hana su kai gudummuwa ko kuma yin aikin su.
7) kungiya ta rubuta ma Chief of Army Staff vBurutai da Mai Girma Gwamnan Katsina takarda bayan tayi meeting da kampanin kera makaman yaki na Nigeria watau Defence Industry Corporation of Nigeria (DICON) tana son ta sayi ma sojojin kasa ma wannan shiyyar, motar hilux guda goma sha biyu (12) masu dauke da bindiga mai jigida, wacce ke kada bishiya, domin girke 3 a tsakani Jibia da Batsari, 3 a tsakanin Batsari da Danmusa, 3 a tsakanin Danmusa da Safana sai ukku a tsakanin Safana – Dutsinma – Kurfi. Muna da yakinin samun wannan motocin zai hana wani shakiyin barawo kawo mamu farmaki da babur sai dai in mahaukaci ne. Su kansu kudin da kampanin ya nema daga garemu sun haura miliyan dari bakwai da arba’in (N740,000,000).
8) kungiyar HESDIN ta kuduri gina security towers dogaye guda shidda a ciki da gefen Dutsinma da kuma kayan aiki na sadarwa, cameras da wuta mai haske don hango mahara koda zasu kawo farmaki.
9) daga karshe kungiyar HESDIN taso in duk wadannan abubuwan suka tabbata, tsaro ya inganta, ta maida yan gudun hijira gidajen su sannan ta basu tallafi domin kama sana’a su ciyar da kansu su zauna cikin mutunci.

Wadannan sune kudurin da kungiyar HESDIN ta saka a gaba wanda duk mai hankali ya san babu su a wannan yankin ko da me kuwa zaice gwamnati nayi. Bamu raina aikin da gwamnati keyi ba haka kuma ba laifi bane muma mu bada tamu gudummuwar kasancewar ita da kanta gwamnatin tace aikin tsaro ba nata bane ita kadai tana neman gudummuwa daga duk mai hali da kishi.

Tabbas kananan kudade basu iya wannan aikin shiyasa muka shiga cikin kasa a duk inda hannun mu zai kai domin neman taimako. In har wani yana kallon yin hakan a matsayin tozarta gwamnati ne to mu ba manufar mu kenan ba. Mu a namu tunanin kare rayuwa tafi muhimmaci da amfani bisa kan jin kunyar duk wani wanda zai ji kunya.

Wannan shine kudurin mu wanda yanzu bashi yiwuwa sanadiyyar batancin da ya shigo cikin aikin daga takardar da dan majalisar Dutsinma ya rubuta ma duniya da kuma sauran zagon kasar da mukayi ta fuskanta wajen masu madafan iko a sunan cewa ina yi ne don neman wani matsayi.
Umar Tata. Tsohon ma aikacin gwamnatin tarayya ne , mai taimakon talakkawa.kuma dan siyasa da ya Nemi takarar gwamnan katsina, har sau biyu. Mun dauko wannan rubutun daga shafin sa na Facebook

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here