An ɗaura auren ɗan shugaban ƙasa da ƴar gidan sarautar Kano ba tare da ganin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ba a wajen ɗaurin auren.

An ɗaura auren Yusuf Buhari da ƴar Sarkin Bichi Zahra Nasiru Ado Bayero a garin Bichi.

Kuma baya ga Sarkin Kano, manyan sarakunan jihar Kano ba su halarci ɗaurin auren ba, ko da yake Sarkin Gaya ya tura wakilinsa.

Sarkin Kano Aminu Ado da Sarkin Bichi Nasiru Ado dukkaninsu ƴaƴan marigayi Sarki Ado Bayero ne.Kuma Sarkin Kano Aminu Ado shi ne babba.

Wasu na ganin Sarkin Kano Aminu Ado ya ƙauracewa ɗaurin auren ne saboda ba a kai ɗaurin auren a Masarautarsa ba, yayin da kuma wasu ke cewa Sarkin ya tsaya ne tarbon baƙi.

Batun ya ja hankali, kasancewar manyan Sarakunan na Kano ƴan gida ɗaya ne. Kuma ɗaurin auren gidan Ado Bayero.

A masarautar Kano aka ɗaura auren ƴar gidan Dangote da kuma ƴar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here