Farfesa Umar Ladbo ya rubuta:

Me Muhammad bin Salman yake nufi?
Kwanakin baya, Yarima mai jiran gadon mulkin Saudiyya, Muhammad bin Salman, ya yi hira da yan jarida inda ya tabo batutuwa dabam-daban dangane da goben masarautar, ciki har da makomarta a matsayin kasa mai aiki da Alkur’ani da Hadisi a matsayin tsarin mulkinta.

Yariman ya yi na’am da Alkur’ani a matsayin tsarin mulkin Saudiyya amma dangane da Hadisi ya ce yana da gyara. Basaraken wanda yake matashi ne mai jini a jika, ya ce ba duk hadisai ya yarda da su ba, shi hadisi “mutawatiri” kawai ya yarda da shi.

Hadisi “mutawatiri” shi ne hadisin da mutane masu yawa suka ruwaito shi, tun daga farkon isnadin hadisin har zuwa karshensa. Hadisi “mutawatiri” shi ne a kololuwar inganci, to amma ba shi da yawa a cikin hadisai. Manyan malaman Hadisi, kamar su Imam Kattani, sun bayyana cewa, a cikin jimillar hadisai ingantattu guda dubu uku (3000) da ake da su, hadisai mutawatirai dari uku (300) ne kawai, watau kimanin kashi daya cikin goma, ko kuma kashi goma cikin dari (10%).

Wannan yana nufin Yarima Muhammad bin Salman kashi goma cikin dari na hadisai ne kawai ya yarda da su, sauran kashi casa’in kuwa ya sa su a kwandon shara. Wannan yana nufin har da hadisan Bukhari da Muslim duka matashin Yariman bai yarda da su ba.

Yanzu abin tambaya shi ne: Mene ne ma’anar wannan? Ma’anarsa shi ne, Muhammad bin Salman ya daura yaki da addinin Musulunci domin addini ba zai taba yiwuwa da Alkur’ani ba kawai, dole sai an hada da Sunna ko Hadisi. Dangane da wannan, Shaihu Muhammad bin Salih bin Uthaimin yana cewa:
“ولو لم يكن سنة لفسد أكثر الدين”
Ma’ana: “Ba don samuwar Sunna ba da yawancin addini ya bata.”

Har yau, matsayin da Yarima Muhammad bin Salman ya dauka yana nufin inkarin Alkur’ani shi da kansa, saboda ai Alkur’ani shi ya yi umarni da bin Sunna. Don haka, wanda duk ya jefar da Hadisi to babu shakka ya saba wa Alkur’ani, kuma ko da ya yi da’awar bin Alkur’ani to da’awarsa ta karya ce. Shaihu bin Uthaimin ya ce:
“من أنكر العمل بالسنة فقد أنكر العمل بالقران”
Ma’ana: “Wanda ya yi inkarin aiki da Sunna to hakika ya yi inkarin aiki da Alkur’ani.”

Don haka a takaice, Yarima Muhammad bin Salman da wannan da’awa tasa ya zama cikin mutanen nan da ake kira “Kur’aniyyun” wadanda da Hausa muke cewa yan Kala-Kato, ko kuma yan Tatsine. Kur’aniyyun, ko kuma yan Kala-Kato, suna hada akidu biyu munana, watau akidar Khawarijawa da akidar Rafilawa yan Shi’a. Imam Abu Sulaiman Alkhaddabi yana fadi a cikin littafinsa mai suna Ma’alimus Sunan, yayin da yake sharhi ga hadisin:
“يوشك الرجل متكئا على اريكته يحدث بحديث من حديثي فيقول بيننا وبينكم كتاب الله عز وجل، ما وجدنا فيه من حلال استحللناه، وما وجدنا فيه من حرام حرمناه، الا وإن ما حرم رسول ألله مثل ما حرم ألله.”
Ma’ana: “Ya kusanta mutum yana zaune a kan shimfida tasa, a ba shi hadisi daga hadisina sai ya ce “Ga littafin Allah nan tsakanin mu da ku, abinda muka samu a cikinsu na halal sai mu halasta shi, kuma abinda muka samu a cikinsa na haram sai mu haramta shi.” Ku saurara! Lallai duk abinda Manzon Allah ya haramta kamar Allah ne ya haramta.”

Imam Alkhaddabi ya ce, wannan hadisi yana gargadi ga barin sabawa Sunnoni wadanda Manzon Allah (SAW) ya sunnanta daga abinda ba’a ambata ba a cikin Alkur’ani, kamar yadda Khawarijawa da Rafilawa suke yi, domin su suna makalewa zahirin Alkur’ani, su kyale Sunna…

Kamar yadda muka ambata a baya, Muhammad bin Salman ya daura yaki da addinin Musulunci kuma yana bisa kan akidu biyu munana. Don haka ya zama wajibi a bayyana halinsa ga Musulmi. Ya zo da mafi munin munkari, saboda haka ya zama wajibi a yi masa inkari.

Koda yake an gabatar da zangazangogi a wasu kashashe Musulmi a kan haka, kamar kasar Tunisia da Pakistan da sauransu. Amma wannan bai isa ba. Wajibi ne a ji muryar malamai ta fito fili domin inkari a kan wannan babban munkari kuma don sauke nauyi da yin nasiha ga Allah da Manzonsa da littafinsa da shugabannin Musulmi da gama-garinsu.

Kuma babu uzuri ga wanda ya ce a yi wa irin wannan shugaba mai wannan ta’asa nasiha a sirri, ko a boye. Wannan sabanin aikin magabata ne. Ina ma jin tsoro kada ya zama boye ilmi, domin munsa’alar tana iya sa jahilai a cikin rudani.

Muna da kyakkyawan misali abin koyi da Imam Ahmad bin Hanbal, Imamu Ahalis Sunna wal Jama’a, Allah ya jikan sa, lokacin da ya tashi tsaye ya yi wa Halifan Musulmi na duniya gaba daya a lokacinsa, watau Alma’amun, nasiha a bayyane dangane da munsa’alar Alkur’ani hatittacce ne ko a’a, kuma ya jure azabtarwa da dauri a kan haka. Da Imam Ahmad bai tsaya tsayuwarsa ta tarihi ba, da yanzu wa ya san yadda akidarmu take. Allah ya jikan Imam Almuzni inda yake cewa,
“عصام الله الأمة بأبي بكر يوم الردة، وباحمد يوم المحنة”
Ko al’umma za ta sake kyankyashe wani Ahamad din?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here