A karshen mako sama da mutane 2000 cikinsu akwai mata da kananan yara gami da tsofaffi suka kaurace wa garin Geidam na jihar Yoben Najeriya. Wani faifan bidiyo da ke yawo a Intanet ya nuna yadda mutanen garin cikin damuwa ke tururuwar barin garin saboda shigar da Boko Haram suka yi garin tun ranar Jumma’a kuma suka ki fita duk da kokarin da sojojin Najeriya suka ce sun yi na fafatawa da mayakan. Shin wace alkibla yaki da ta’addanci ke dauka a Najeriya ganin cewa a yayin da ake gwabza fada da Boko Haram din a Geidam kwatsam kuma sai aka ji an kai wa garin Mainok na jihar Borno hari?

A lura👉hotunan da ke kasa tsofaffi ne!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here