Advert
Home Sashen Hausa MAULUDI: Daga Unguwar Manna Filin bugu zuwa Kwanar Chake a garin Katsina...

MAULUDI: Daga Unguwar Manna Filin bugu zuwa Kwanar Chake a garin Katsina…

MAULUDI: Daga Unguwar Manna Filin bugu zuwa Kwanar Chake a garin Katsina…

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 

Yau Litanin, 18/3/1443 daidai da 25/10/2021, wasu Unguwanni na Birnin Katsina suka tashi, da wani abin Mamaki, da ba a saba gani ba, a yankin,

Tun daga Marnar gangare, Filin Bugu/Gambarawa, zuwa Kwanar Chake, da ake kira Kasuwar HIMATA, mutanen yankin suka shirya wani gagarimin Mauludin Annabi, S.A.W wanda sukace shine na farko, a yankin, taron Mauludin ya kasu Da’ira-Da’ira, Masu karatun, Qur’ani, masu Ishiriniya, Masu Diwani, da Sha’irai, ko ina busa Titin, da shiga ta fararen  kaya, cikin farin ciki,

Wani yanki na masu karatun Alqur’ani mai girma a wajen bikin Maulud

Inda gidaje da shagunan da ke yankin suka shirya wa baki da ‘yan unguwa kyaututtuka abinci da lemuna, da da turare.

Baki manyan malamai da ‘yan siyasa, sun halarci wajen Inda Idon Katsina City News dake wajen ya hango Danmajalisar katsina Hon Ali Abu al’baba, daraktan SEMA, Hon. Babangida Nasamu,

Duba da cewa wannan unguwa kusan itace Cibiyar da ta hada manyan makarantu Islamiyyu da suka kasance jigo a taron Mauludi da ake gudanarwa na jiha baki daya, kuma unguwar tana da rassa na manyan Malaman da suka Assasa zagayen Maulud a Katsina, mukaga dacewa a shirya wani Maulud na zumunci, da soyayya da zai kara hada kan dukkanin wadannan Unguwanni, kuma kwamiti ne na musammn muka samar da zai dunga shirya wannan Al’amari duk shekara insha Allah…..inji wani daga cikin ‘yan kwamiti da muka zanta dashi

 

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...