Advert
Home Sashen Hausa MAULUD: 'Yan shi'a sun yi fitar kwarin ɗango a Katsina...

MAULUD: ‘Yan shi’a sun yi fitar kwarin ɗango a Katsina…

MAULUD: ‘Yan shi’a sun yi fitar kwarin ɗango a Katsina…

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Yau Talata 12 ga watan Rabi’u Awwal da tayi dai-dai 19 goma, 2021 ‘yan shi’a a katsina sun fito kwansu da ƙwarƙwatarsu domin bikin murna da zagayowar Rana da watan da aka haifi Fiyayyan Halitta Annabi Muhammad (S)

Kamar ko wace Shekara ‘yan shi’ar Al’majiran Sheikh Ibrahim El’zakzaky sun saba fita a duka fadin Najeriya a ranar sha biyu ga watan suna bukukuwa da nuna farincikinsu, “Yau rana ce da aka haifi Fiyayyan Halitta shiyasa muka fito mu nuna farinciki da samuwar Annabi, wanda shine ramzi na hadin kai, shi yasa muka fito maza da mata kabilu mabanbanta domin taya Annabi murna da farantawa Allah (T) akan Masoyinsa” Inji wani da katsina City News ta zanta dashi

Zagayen na Maulud da ya fara, a garin na katsina tun misalin karfe 9 na safe,daga Unguwar Madawaki, ya bi ta marnar gangare zuwa kofar ‘yan daka, ya dauke hanya zuwa Rafin dadi, yabi ta Mobil ya hau babban titin kofar Durbi inda aka yanke hanya zuwa filin Samji, inda makarantu daban daban suka yi faretin girmamawa ga Annabi (S) a karshe Malam Shehu Dalhatu, yayi jawabi na taya murna ga Al’umar musulmi, taron ya karkare da misalin karfe hudu na yamma acikin farin ciki da raba wa al’uma alawa da kayan marmari duka dai Albarkacin Annabin (S)

 

 

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yansanda A Katsina Sun Chika Hannu Da Yan Kungiyar Asiri Biyu

Rundunar Yan Sanda Ta Jihar Katsina ta kame wasu matasa biyu da make zargin yan Kungiyar Asiri ne. Kamar yadda Jami'in Hulda da Jama'a na...

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...