Shahararren malamin nan na addinin Muslunci kuma shugaban darikar tijjaniyya na Afrika Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa yin maulidi bin umarnin Allah ne.

Malamin yayi wannan kalaman nasa ne acikin wani wa’azin sa inda Shehin Malamin ke cewa: “Idan kaji mutum yana sukar maulidi kace masa ai maulidin iri biyu ne:

1 – Da farko akwai maulidi na zamani wato watan (Rabi’ul Awwal) wannan shine maulidi na zamani.

2 – Akwai kuma maulidi na makani (Wuri) wato Makkah da Madinah.

Shehin yaci gaba daa cewa: Idan mutum ya samu kudin zuwa Hajji zai tafi dolensa, shin anan waye ya kira shi,? Malami ya tambaya.

Aka ce: Allah S.W.T ne ya kira shi.

Sai Shehin Malamin yace “to duk wanda ya tafi Makkah da Madinah to ya tafi maulidin Manzon Allah (S.A.W) ne na Makani zai je dan ya ga inda aka haifi Annabi (S.A.W) ya ga masallacin sa, ya ga gidan sa sannan ya ga abubuwan da Annabi (S.A.W) yayi rayuwa da su.

Don haka dole ne Musulmi yayi maulidi ko na Makani wato (Makkah da Madinah), ko na zamani din wato watan (Rabi’ul Awwal) Allah ya barmu da son Annabi (S.A.W).” Inji Malamin.

Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here