Daga Kamalancy

Laftanar Dairo Mutumin dake acikin jirgin da barayin daji suka harbo yayi ƙoƙarin samun tsira da ranshi alokacin afkuwar iftila,in

A wasu rahotanni damuke samu Sun ce, Laftanar Dairo ya gudanar da aikin ne cikin ƙoƙari da hazaka kuma ya kashe barayin daji da ‘yan bindiga da,dama kafin lokacin afkuwar lamarin.

A kan hanyarsa ta komawa sansaninsa, ne lokacin da wasu gungun ‘yan fashi suka dirar wa jirgin suka samu yin galaba akan shi.

Ayanzun haka Laftanar Dairo yana cikin koshin lafiya, kuma ya bayyana cewar nan bada jumawa ba insha Allahu dole ne a ci gaba da gudanar da wannan aikin.

Muna masa addu,a da fatan Alkhairi allah yaƙara taimakon ku akan yan ta addan daji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here