Advert
Home Sashen Hausa MATSAYAR MU; TSAKANIN JAM'IYYAR APC DA JARIDAR TASKAR LABARAI

MATSAYAR MU; TSAKANIN JAM’IYYAR APC DA JARIDAR TASKAR LABARAI

MATSAYAR MU; TSAKANIN JAM’IYYAR APC DA JARIDAR TASKAR LABARAI

Sharhin Hukumar Gudanarwa

Sakamakon wasu labaran da muke rubutawa a kan wani jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, wasu sun dauka ko jaridar na da wata jikakka ne da jam’iyyar ko shugabanninta.

Wannan ya sa wasu na tambaya, wasu na rubuto wasikun neman jin ko akwai wata azazza?

Hukumar Editocin jaridar sun yi zama a jiya Litinin 28/12/2020, inda suke son jaddada matsayar cewa; Jaridar Taskar Labarai ba ta da wata ajanda ga jam’iyyar ko wani cikin shugabanninta.

Duk labaran da jaridar ta ba da a kan jam’iyyar ko wani daga cikin shugabanninta, sai da aka bi duk ka’idar dokar aikin jarida kafin a fitar da shi, kuma aka tabbatar abin da aka rubuta za ta iya kare shi a ko’ina aka gayyace ta.

A shekarar 2020, jaridar ta yi rahotanni 1540, guda 700 a kan tsaro ne, sai wasu a kan nisahdi da sauran al’mmura, 11 ne kacal ne ga jam’iyyar APC ko a kan wani Shugabanta.

Jaridar ta jawo hankalin masu rike da mukamai ko dai a ofishin jam’iyya ko na gwamnati. Su sani labari a kansu yana daga cikin aikin jarida.

Don haka duk wani mai rike da mukamin jam’iyya in har ya yi abin labari, za mu bi ka’idar aikinmu, kuma mu yi labari a kansa.

Don haka in mutum bai so a yi labari a kansa, to ya ajiye mukamin da yake rike da shi, wanda yake amfani da shi wajen cimma bukatarsa.

Wasu shugabannin na APC ko sun ajiye mukamansu, suna da sauran kallo, don wasu hukumomin kasa da kasa da na tsaro suna nan sun yi bakam, jira kawai suke.

A irin wannan yanayin ko mutum ya ajiye aikin, in aka zo ana tuhuma da bincike, za mu rika ba da labari abin da ke faruwa. Don kowa ya debo da zafi, bakinsa.

Ko ana tuhumar mutum, in mun ga ana shirin wuce gona da iri, ko za a zalunce shi, za mu tsaya masa da rubutunmu. Don ba mu son zalunci ko daukar alhaki.

Muna kara jaddada cewa ba mu da komai ko wata tsattsama da jam’iyyar APC ko shugabanninta, aikinmu kawai muke kamar yadda ka’ida da doka ta tanada.

Ba ruwanmu da tsarin rayuwar mutum ta kashin kansa, misali a ce yana neman mata ne a asirce. Wannan shi da Ubangijinsa, amma in ya shafi matar aure ko karamar yarinyar da ba ta mallaki hankalinta ba, in muka sani za mu bincika, in mun tabbatar za mu ba da labari, amma wasu tsare-tsaren rayuwar mutum da ya tsara wa kansa, duk babu ruwanmu.

Labari da ya shafe ka kuma yake danganta da al’umma da hakkinsu ya rataya a kanka, za mu ci gaba.

Don haka jaridar nan za ta ci gaba da ba da labarin jam’iyyu ciki har da APC a kanta da shugabanninta, don jam’iyyu sune ruhin mulki a dimokaradiyya.

Allah ya sa mu da mu dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yakamata a saka Jihar Katsina cikin jihohin da ake bawa Tallafi domin fuskantar ƙalubalen tsaro……Aminu Bello Masari ga Gwamnatin Tarayya

Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yayi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saka jihar Katsina cikin jihohin da take ba tallafi...

Kungiya Mai Fafutukar Ganin An Samu Sabuwar Jahar Katsina Mai Suna Project New Katsina Sun Ziyararci Radio Najeriya Companion FM reshen Jahar Katsina

*Kungiya Mai Fafutukar Ganin An Samu Sabuwar Jahar Katsina Mai Suna Project New Katsina Sun Ziyararci Radio Najeriya Companion FM reshen Jahar Katsina* Daga Zahraddeen...

BALA ABU MUSAWA NE ZABINMU ~~~Gamayyar Kungiyoyin Goyon Bayan APC na Shiyyar Daura

Daga Bishir Mamman @ katsina city news Kungiyar wadanda suke da wakilci a kananan hukumomin yankin sanatan Daura, karkashin shugabancin Sani Abdurrahman da mataimakiyarsa Hadiza Mamman. Suna...

POLICE ARREST SEVEN FOR KIDNAP, INFORMANTS.AND SUPPLY OF FUEL

Hassan Male @ Katsina city news The Katsina State Police Command had on the 18/9/2021 succeeded in arresting one Lawal Shu’aibu ‘m’ aged 32 years of...
%d bloggers like this: