Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina QS Mannir Yakubu ya karbi bakuncin ministan harkokin wutar lantarki Alh Aliyu Abubakar da yan tawagar shi a ofishin shi dake fadar gwamnatin Jihar Katsina Muhammadu Buhari House yau 31/12/2021.

Ziyarar nada nufin bayyana ma Gwamnatin Jihar Katsina muhimman abubuwan da suka kawo shi Katsina da suka hada da duba yan sauran ide iden aikin wuta mai amfani da iska dake lambar rimi, tare da duba yadda za’a kara ma wutar karfin mega wat, ta hanyar amfani da hasken rana bayan amfani da iskan, ta yadda zata zamana ta amfanar fiye ga yadda aka kudirta a farkon kirkirarta. Hakanan kuma MINISTAN yayi bayanin inganta harkokin wutar Katsina da daura.

Alh Aliyu Abubakar ministan harkokin wutar lantarkin ya yaba ma wakillan tawagar zauran dattawan Katsina bisa ziyarar shi da sukayi a ofishin shi suka gabatar da rokon su da ofishin MINISTAN da ya sanya wasu garuruwa na Katsina acikin garuruwan da Gwamnatin tarayya zata sanya ma wutar lantarki.

Idan dai mutane basu mantaba zasu iya tuna ziyarce ziyarcen da mataimakin Gwamnan Jihar Katsina yasha kaiwa a wannan ma’aikatar a karkashin hukumar da yake jagoranta ta bunkasa matsakaita da kananun masana’anti ta jihar Katsina da niyyar rokon ofishin ma’aikatar wutar lantarki ta kasa da yazo ya ida kammala wannan aikin na wutar lambar rimi tare da kawo ma Jihar wasu ayyukan daga ma’aikatar don bunkasa harkokin kasuwanci a fadin Jihar Katsina da inganta jin dadi da bunkasa walwala da rayuwar al’ummar Jihar Katsina.

A jawabin Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ya yaba tare da jinjina ma ministan tare da yan tawagar shi bisa ziyarar aiki da suka kawo a Jihar Katsina tare da addu’ar Allah yasa suyi ayyukan su lafiya ya kuma maida kowa gidajen su lafiya.

A cikin wadanda suka tarbi ministan da yan tawagar shi akwai Sanata Abba Ali Katsina tare da wasu wakillai daga Katsina da daura na zauren majalissar dattawan Jihar Katsina da tsohon Gwamnan Katsina da sokoto na soja akwai kwamishinan yada labarai na Jihar Katsina Alh Abdullareem Sirika, da SA Power, da babban sakataren ofishin Mataimakin Gwamnan Alh Aminu Abu bazariye, akwai shugaban hukumar saka hannun jari na Jihar Katsina Katsina State Investment Promotion Agency (KIPA) Alh Ibrahim Tukur Jikamshi da dai sauran su

Muhammad Barmo Hadimi Na Musamman Ga Mataimakin Gwamna Akan Sabbin Kafafen Sadarwa da Yada Labarai (New Media)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here