MATSALAR WUTAR NEPA A KATSINA: Yakamata ayi zaman Sulhu- Sheikh Yaqub Yahaya a wajen rufe Tafsir

Sheikh Yaqub Yahaya katsina Malamin Addinin Musulunci; Yayi wannan tsokacin ne a wajen rufe Tafsirin Al’qur,ani me girma na watan Ramadana a bana da yake gudana a Muhallin’yan uwa musulmi dake unguwar ɗaki tara a garin Katsina.

Sheikh yace “Yakamata ne ita hukuma ko kamfanin samar da wutar lantarki su zauna da ‘yan unguwa suji korafin juna, Nepa su faɗi korafin su, suma ‘yan unguwa su fadi korafinsu, sai a cimma matsaya. Wannan shi ake cema sulhu.

Yace amma sun shiga unguwannin mutane sun ɗage Taransifomomi da wanda ya biya da wanda be biya kudi ba matsalar kowa ta shafe shi, don haka shi wanda ya biya ba’aimasa adalci ba. Yace idan sulhun yaki yi yuwa sai al’uma suyi hakuri da wutar akalla na tsawon wata uku su daina biyan kudin su hakura sai muga idan Kamfanin zaici gaba batare da mutane ba, su kuma sai su aje wutar su tunda haka suke so, su kuma waɗanda suka biya (kamar yanda sukace anaso mutum ya biya kashi sittin cikin dari) sai su tattara hujjojin su su tafi kotu domin bin haƙƙoƙin su, tunda su basu tausayawa al’uma ba du da irin wannan musibar zafi ga azumi ga sauro ga yara ƙanana amma hakan baisa sun tausaya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here