Matasa 554 ne suka kammala koyon aikin Dansanda kuma suka shirya tsaf domin fara aikin a karkashin shirin shigar da al’umma cikin harkar tsaro (Community Policing) a fadin wannan jiha.

Wannan horo da akayi masu na koyon aikin Dansandan anyi masu shi ne a Kwalejin Horas da’Yan sanda (Police College) dake Kaduna.

A cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isa ya bayar, ya bayyana cewa za a tura su zuwa cikin al’ummomin da suka fito domin kama aiki.

Ya kara da cewa suna da karfin iko irin na ‘Yan sanda kuma za su rika sa kaya tare da yin aiki tamkar ‘yan sandan, iyaka dai ba za su rika amfani ba da bindiga da kuma abinda ya shafe ta.

Da yake masu jawabi bayan kammala samun wannan horo, Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Katsina Alhaji Sanusi Buba yace za suyi aiki kafada da kafada da ‘yan sanda, sannan yayi kira gare su dasu zama masu gaskiya, ɗa’a tare da sadaukarwa a cikin aiki domin rage yawan aikata laifuka da kuma samar da tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here