Advert
Home Sashen Hausa MATSALAR TSARO~ Burtaniya Za Ta Shigo Najeriya Dan Yakar Ta'addanci

MATSALAR TSARO~ Burtaniya Za Ta Shigo Najeriya Dan Yakar Ta’addanci

MATSALAR TSARO~ Burtaniya Za Ta Shigo Najeriya Dan Yakar Ta’addanci

Gwamnatin Burtaniya ta nemi gwamnatin Najeriya ta bata damar shigowa Najeriya don ganin bayan ‘yan ta’adda da suka addabi kasar

Burtaniya ta nuna damuwa game da kara tabarbarewar harkokin tsaro a Najeriya tare da neman ba da tata gudunmowar domin dakile matsalar tsaron.

Babbar jakadiyar Burtaniya a Najeriya Catriona Laing ce ta bayyana hakan, tana mai cewa Landan ta ƙagu ta kawo wa Najeriya dauki a yakin da take fama da ta’addanci.

Jami’ar ta ce “Mun yi matukar damuwa game da tabarbarewar yanayin tsaro a wannan kasar.

“Ina nufin Najeriya na fuskantar matsaloli da dama a ko ina – Arewa Maso Gabas ‘yan ta’adda, a Arewa Maso Yamma na fama da ‘yan bindiga, a Arewa ta Tsakiya kuma matsalar manoma da makiyaya, a Kudanci matsalar tsagerun Neja Delta ko ina ana fama.

Laing ta ce Burtaniya ta yi ta kokarin taimakawa ta hanyar bai wa sojojin Najeriya atisaye, da kuma shirin yadda za su rika cire abubuwan fashewa.

Shin a matsayin ka na dan Najeriya ka gamsu su shigo Najeriya?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?….Siyasar zaben 2023

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM'IYYAR APC? . ..Siyasar Zaben 2023 Mu'azu Hassan @ Katsina City News Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan...

Bikin bada sandar girma a Masarautar Rano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya Jagoranci mika sandar Girma ga Mai Martaba Sarkin Rano, Amb. Alh. Kabiru Muhammad Inuwa Autan...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Nada Amina Muhammad Daga Jihar Gomben Najeriya Karo Na Biyu

Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa. An sake...

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021 DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya...
%d bloggers like this: