Matsalar tsaro: A koma ga Allah a ci gaba da istigifari – Bala Lau

..

Shugaban Ƙungiyar Izala a Najeriya, Sheik Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su koma ga Allah ta hanyar istigifari domin samun sauƙin ƙalubalen tsaro.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta JIBWIS ta fitar a shafinta na Facebook, ta ambato shugaban yana bayar da umarni ga limamai da su duƙufa da addu’o’in Al-Qunut a faɗin ƙasar domin samun sauƙi daga Allah.

Sheik Bala Lau, ya buƙaci gwamnatoci a dukkan matakai da jami’an tsaro su yi iya bakin ƙoƙarinsu wurin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Wannan kiran na shugaban Izalan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan sace sama da ɗalibai 500 a Ƙanƙara da ke jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here