Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira da a taimaka wa marayu a faɗin ƙasar, yana mai cewa akwai buƙatar a yi wa ɗan Adam hidima.

Osinbajo ya lura cewa zama maraya baya tantance girman makomar yaro. Ya ce manyan mutane da yawa a Najeriya da duniya marayu ne, saboda haka akwai buƙatar a taimaka wa yara a gidan marayun.

Mataimakin shugaban ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da wata cibiyar sadaka da ci gaban zamantakewa, mai suna Dorian Home a Akure, babban birnin jihar Ondo, ranar Alhamis. Wani mai taimakon al’umma, Dr Tolulola Bayode ne ya gina wannan cibiya.

A cewarsa, adadin zawarawa da marayu a Najeriya ya karu saboda matsalolin rashin tsaro, kamar tashin hankali da rikice -rikice a sassan ƙasar da dama.

Osinbajo ya ce, “Muna fuskantar babban ƙalubale. A cikin 2015, Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma ta Tarayya ta kiyasta cewa akwai marayu da yara marasa galihu kusan miliyan 17.5 a cikin ƙasa mai mutane miliyan 200. Wannan yana kusa da kashi tara na yawan jama’a. Abin baƙin ciki, wannan adadin ya ƙaru a cikin shekaru saboda tashin hankali da rikice-rikicen al’umma a sassa daban-daban na ƙasar.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya ce sabon aikin jin ƙai da aka ƙaddamar zai cika kyawawan manufofin gwamnatinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here