Matashi ya kashe mahaifiyarsa da mahaifinsa da ƴan uwansa

..

Wani ɗalibi na jami’ar Kenya, ya shaida wa ƴan sandan ƙasar yadda aka yi ya kashe mahaifansa da ƴan uwansa.

Kafafen yaɗa labarai a ƙasar sun ruwaito cewa Simon Warunge, mai shekara 22, ya yi amfani da sandar ƙarfe inda ya buga wa mahaifiyarsa da mahaifinsa da ƴan uwansa biyu, kafin daga baya ya caccaka musu wuƙa suka mutu.

Ɗalibin ya shaida wa ƴan sanda cewa iyayensa ba su da imani shi ya sa ya yi musu haka, kamar yadda jaridar Star a ƙasar ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa sun ɗora masa karan tsana kuma suna gulmarsa, kamar yadda Citizen TV ta ruwaito yana cewa.

Sai dai ƴan uwansa mata biyu waɗanda suka dawo daga makaranta sun tsira daga wannan harin.

Kafin rasuwar mahaifiyarsa, ta kasance malamar jinya a asibitin masu taɓin hankali a Kenya, inda shi kuma mahaifinsa ya kasance malamin jinya a Amurka, kuma ya koma ƙasar ta Kenya ne domin bikin Kirisimeti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here