MATASAN PDP SUN FARA KOYON HARBI DA BAKAN DANKO

 

Daga shafin Kwamrad Iliya

Ƙungiyar Katsina state PDP Social media organisation ta ƙaddamar da Atisayen Harbin Danko(Operation catapults shoot)

Biyo bayan kiran da gwamnan jahar Katsina ya yi Rt Hon Aminu Bello Masari na cewa al’ummar jahar Katsina su nemi bakan danƙo(Catapults) domin kare kansu daga harin yan bindiga.

Shugaban ƙungiyar PDP Social media organisation Comrd Nuraddeen Adam Kankara Tina ya jagoranci wasu daga cikin ƴaƴan ƙungiyar wajen ƙaddamar da Shirin koyon Harbin Danko a cikin birnin Katsina.

Shugaban ƙungiyar yace sun bi umarnin gwamnatin jahar Katsina ne na koyon harbin kuma zasu cigaba da fadada horon har zuwa kananan hukumomi jahar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here