Matar da ta ƙirƙiri taliyar Indomie ta rasu

Indomie

Matar da ta ƙirƙiri taliyar Indomie ta rasu tana da shekara 59 a duniya.

An samu rahoton rasuwar Nunuk Nuraini ne a ranar larabar makon nan, wadda ta yi aiki a matsayin manaja a wani kamfani a Indonesia na kusan shekara 30.

Da yawa suna ta yabon ta kan wannan bajinta da ta yi.

Indomie ta mamaye duka sunayen wata taliya mai irin wannan tsari na ta a Indonesia, inda mutane da yawa suka mayar da ita babban abincinsu na yau da gobe.

Amma a ‘yan shekarun baya-bayan nan ta zama wata fitacciyar abinci a duniya, tana kuma kara karbuwa ba kawai a Kudu maso Gabashin Asia ba, har ma da kasashen Australia da Najeriya.

Duk da cewa kamfanin na da gwamman abubuwa da yake samarwa, amma “mi goreng” ko kuma taliyar Indomie ita ce ta fi shahara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here