Wani mataimakin shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa, DCG Alhaji Usman Ndagi ya rasu a Abuja bayan awanni 18 da rasuwar ƙanwarsa a jahar Neja.

Alhaji Usman Ndagi DCG Immigration officer

Alhaji, wanda dan asalin garin Mokwa ne a jahar Neja ya rasu a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba bayan samun labarin rasuwar yar uwarsa a ranar Laraba, 18 ga wata.

Kakaakin hukumar Immigration, DCI Sunday James ya tabbatar da mutuwar Alhaji, inda ya bayyana rashinsa a matsayin lamari mai matukar ban mamaki.

“Labarin da na samu shi ne Alhaji ya rasu ne bayan samun labarin rasuwar yar uwarsa, mutumin kirki ne mai riko da addini, wanda yake yawan zuwa Masallaci Sallah.” Inji James.

Wani dan uwansa, Yax Mokwa ya bayyana cewa mamacin ya rasu ne bayan ya yi korafin cewa yana ganin jiri yayin da ake shirya masa kayansa don tafiya jana’izar yar uwarsa a jahar Neja.

“Mutuwar yar uwar tasa ya kada shi matuka, don haka ya shirya don kama hanyar zuwa Mokwa daga Abuja domin halartar jana’izar.

“Ya bada umarnin a kai masa jakarsa mota saboda yana dan jin jiri haka saboda haka zai dan huta kadan, daga nan sai gawarsa aka mayar gida.” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here