Siyasar Zamfara ta ɗauki sabon salo, yayin da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ɗin ke ƙoƙarin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu, bisa zargin ya shirya taron siyasa a lokacin da ake cikin alhinin hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

An kuma zargi Aliyu da nuna rashin ɗa’a da cin mutuncin Kwamishinan ‘Yan Sandan Zamfara a wani saƙon tes da su biyun su ka yi wa juna.

Ana raɗe-raɗin cewa ‘yan Majalisar Dokoki na shirin yin amfani da waɗannan dalilai su tsige Aliyu, wanda ya ƙi bin Gwamna Bello Matawalle canja sheƙa zuwa APC.

Majalisa ta nemi Aliyu ya bayyana a gaban ta ya bada ba’asin dalilin da ya sa ya yi taro da kuma bijire wa shawarar da jami’an tsaro su ka ba shi.

Sun ce abin da Mataimakin Gwamnan ya yi abu ne mai iya zafafa matsalar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Zamfara.

Kakakin Majalisar Aliyu Magarya ya tabbatar da aika takardar gayyatar kuma ya ce “abin da Mataimakin Gwamna ya yi ba daidai ba ne.

Mamba mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Maru ne ya gabatar da roƙon a gayyato Mataimakin Gwamnan.

Yusuf Alhassan ya zargi Mataimakin Gwamnan da ƙoƙarin haddasa tashin hankali a jihar.

Sai dai Mataimakin Gwamnan ya ce har yau bai amshi takardar gayyatar ba, domin ba ta kai wurin sa ba.

An dai nuno Mataimakin Gwamnan a cikin wani bidiyo ya na cewa babu wanda ya isa ya hana shi shiga Zamfara.

Majiya: Premium Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here