Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu FNIQS ya wakilci Gwamna Masari wajen bukin kaddamar da littafin shehin malamin nan na Madina wato ibn FARHUN da wasu malaman jami’ar Bayero (BUK)suka fassara zuwa harshen hausa.

Shahararren attajirin nan dan kasuwa da ya kwashe shekaru casa’in da hudu 94 a duniya cikin koshin lafiya wanda yake a garin Kano wato Alhaji Aminu Alhassn Dantata ne ya dauki nauyin buga littafin mai suna TABSWIRATUL- HUKKAM na Sheikh ibn FARHUN da aka fassara ya zuwa harshen hausa.

Taron dai ya samu halartar sarkin musilman najeriya Amirul Mumineen Mai alfarma Alh Sa’ad Abubakar Sa’ad na uku da mai martaba sarkin katsina Alh Abdulmumeen Kabir Usman da ya samu wakilci, da mai Martaba sarkin daura Alh Umar Faruk Umar, da Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero, da sarakunan daga sassan najeriya da makwafta da yan kasuwa, da yan siyasa da dai sauran su.

Littafin zai taimaka ma alkalai da lauyoyi zai kuma taimaka wurin saukin koyar da fannin ilimin shari’a a jami’o’in koyar da aikin shari’a, da kuma lauyoyi da kuma wurin aiwatar da shari’ar da lauyancin. Haka kuma zai taimaka ma harkokin shari’a a kasashen afrika baki daya.

A fassarar littafin anyi amfani da manyan sanannun kwararru masana fannin shari’ar musulunci tare da binciken kwakwaf wajen fassara littafin domin saukaka fahimtar shi cikin sauki.

A jawabin gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jinjina ma shahararren Dan kasuwa Alh Aminu Al-hassan Dantata bisa jajircewar shi wurin daukar nauyin fassara wannan littafi dama sauran littattafan da ya dauki nauyin fassarawa da wadanda yake da niyyar daukar nauyin fassara su domin amfanuwar al’umma baki daya.

Haka zalika Gwamna Ganduje ya kara jinjina ma kokarin shehunnan malamai masana da suka tattaru suka bada gudummuwar su wurin aiwatar da wannan gagarumin aikin na ciyar da harkokin shari’a a gaba da kasa da afrika baki daya.

Mai Martaba sarkin musulmai Alh Sa’ad Abubakar na uku yace a cikin kokarin da akayi don bunkasa harshen hausa an fassarar littattafan musulunci guda 120 daga cikin 312 da sheikh Usman bin fodiyo ya rubuta da Abdullahi gwandu.

Alh Sa’ad Abubakar Sa’ad ya kara da cewa yanzun haka a jihar sokoto suna ta kokarin shirye shiryen hada gwuiwa tsakanin jami’ar Usman Danfodiyo da Jami’ar bayero university ( BUK) domin gina cibiyar koyo da nazarin fassarar littattafan musulunci da aka rubuta da larabci ko wani yare zuwa harshen hausa.

Wanda ya dauki nauyin fassarar littafin kuma babban mai kaddanar da littafin Alh Aminu Al-hassan Dantata yayi godiya ga Allah madaukakin sarki bisa iko da ya bashi na so da kaunar ciyar da harkokin addinin musulunci a gaba.

Alh Aminu Dantata yace insha Allahu zai ci gaba da daukar nauyin fassara dukkan littattafan addinin musulunci zuwar harshen hausa har tsawon rayuwar shi, domin amfanuwar al’ummar hausa da ciyar da addinin musulunci agaba.

Saboda muhimmancin wannan littafin da aka fassara zuwa harshen hausa mai suna TABSWIRATUL HUKKAM ga cibiyoyin shari’a Gwamnatin Jihar katsina ta sayi wasu kwafi na littafin akan kudi naira milyan biyar ta hannun wakilin Gwamna Masari wato Mataimakin Gwamnan jihar katsina Alh Mannir Yakubu a lokacin kaddamar da littafin.

Lokacin da babban mai kaddamar da littafin Alh Aminu Dantata da gwamnatin jihar kano suka sayi wasu kwafi kwafi akan kudi naira milyan hamsin hamsin hamsin.

Shahararrun yan kasuwa na duniya da suka fito daga kanon Alh Aliko dangote da Alh Abdussamad Ishaka Rabiu ( BUA ) sun sayi wasu kwafi kwafi akan kudi naira milyan talatin talatin da dai sauran su.

Iyalai da yaya da jikokin Alh Aminu Dantata sun sayi wasu kwafi kwafi na littafin akan milyoyin kudade hakanan wasu al’ummar garin kano da makwafta yan kasuwa da dai sauran su sun sayi kwafi kwafin littafin akan milyoyin kudi.

Taron ya gudana a babban dakin taro na jami’ar B. U. K dake cikin garin kano.

Muhammad Barmo Hadimi Na Musamman Ga Mataimakin Gwamna Akan Sabbin Kafafen Sadarwa Da Yada Labarai ( New )

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here