Advert
Home Sashen Hausa Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alh Mannir Yakubu ya karbi rahoton kwamitin gudanar...

Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alh Mannir Yakubu ya karbi rahoton kwamitin gudanar da babban taron tattaunawa kan batun tattalin arziki na jihar Katsina da za a gudanar.

Babban daraktan hukumar bunkasa saka jari ta jiha Alh Ibrahim Tukur Jikamshi ne ya jagoranci mambobin kwamitin wajen gabatar da ruhoton.

Da yake karbar ruhoton, mataimakin Gwamnan ya baiyana cewa taron na bana ya sha bambam da na baya sabili da muhimman batutuwa da ya dauka domin tattaunawa a kan su.

Wadannan batutuwa kuwa a cewar sa sun haɗa da gina cibiyar masaku ta funtua da kuma da ke a kan hanyar zuwa Jibiya.

Alh Mannir Yakubu ya jinjina wa kwamitin wajen gudanar da aikin sa domin tabbatar da yiwuwar taron cikin nasara tareda nuna godiyar sa ga kamfanoni da hukumomin gwamnati da suke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatuwar taron.

A jawabinsa babban daraktan hukumar bunkasa saka jari ta jiha Alh Ibrahim Tukur Jikamshi yayi waiwaye akan batutuwan da aka tattauna a wancan taron gamida nasarar da aka samu.

Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya kuma yi bayani a kan yadda aka tsara taron na bana daga ranar farko har ya zuwa ranar da za a kammala shi, sannan yayi godiya ga kamfanoni da hukumomin gwamnati bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatin jihar Katsina wajen gudanar da ayyukan ci gaban al’ummar ta.

Muhammad Barmo Hadimi Na Musamman Ga Mataimakin Gwamna Akan Sababbin Kafafen Sadarwa Da Yada Labarai (New Media) 7/10/2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: