Masu Zanga-zanga Sun Tare Hanya Tare Da Kone-kone A Abuja

Rahotannin da ke shigo mana daga Abuja sun nuna cewa, mazauna garin Gauraka, Dumez, da Gwazunu sun tare babbar hanyar arewacin Kano Kaduna Express Way suna zanga-zanga tare da kone-kone domin nuna bacin rai sakamakon yanda satar mutane ta yawaita a Yankunansu.

Lamarin ya haddasa cunkoson ababen hawa, mayan motoci da mashina sun tsaya cak a ya yin gudanar da zanga-zangar.

Masu zanga-zangar sun nuna bacin ransu sakamakon yanda masu satar mutane suka addabin Yankunan nasu, suna karbar kudin fansa tare da muzgunawa al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here